✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 4 sun mutu a hatsarin mota a Neja

Motar ta fadi ne a sakamakon gudun wuce hankali.

Mutum hudu ne suka riga mu gidan gaskiya sannan uku sun jikkata a hatsarin motar da ya auku ranar Lahadi a Jihar Neja.

Hatsarin a cewar Kwamadan Hukumar Kiyaye Hadurra reshen jihar, Kumar Tsukwam, ya auku ne da daddare kusa da kauyen Nami da ke Karamar Hukumar Agaie ta jihar.

Ya ce motar da lamarin ya shafa, ta dauko kayan sunadarai ne da kuma fasinjoji 49 daga Legas da nufin zuwa Kano.

“Mutum 49 (duka maza) hatsarin ya ritsa da su inda hudu suka mutu nan take, uku sun jikkata sannan 42 sun tsallake rijiya da baya.

“An kwashi wadanda suka ji rauni da ma gawarwakin zuwa Babban Asibitin Lapai,” in ji Tsukwam.

Ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon gudun wuce kima da direban motar ya yi wanda hakan ya sa motar ta kwace masa ta fadi.

(NAN)

%d bloggers like this: