Akalla mutane 30 ne ake fargabar sun nutse a ruwa a lokacin da suke kokarin tsere wa ’yan bindiga daga kauyen Birnin Waje da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, harin da ’yan bindigar suka kai kauyen a daren Laraba ne ya sanya mata da kananan yara suka nufi gabar Kogi domin tserewa a Kwale-Kwale.
- Ana binciken kisan ma’aurata da jaririyarsu ’yar wata 8 a California
- Dan wasan Chess da ake zargi da magudi ya yi biris da martanin mutane
To sai dai bayanai sun ce yawan da suka yi wa Kwale-Kwalen biyu, ya sa ya kife da su a ciki.
Wani da ya sha da kyar bayan harin, Babangida Bukkuyum, ya ce ’ya’yan kanwarsa uku na cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
“‘Yan bindigar sun bi mutanen da ke gudun tsira da rai har bakin kogin suna harbe-harbe, hakan ya sa matuka kwale-kwalen suka fada cikin ruwan suka bar kwale-kwalen da mutanen ke ciki don tsira da rayukansu.
“Duk da wasu daga mtanen sun tsira bayan sun yi iyo zuwa gabar kogin, wasu har yanzu ba a san in da suke ba.
“‘Har yanzu kuma akwai fargabar ‘yan bindigar na nan a yankin, don abin da ma ya kawo cikas ga ceto mutanen kenan”, inji shi.
Duk yunkurin da muka yi domin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘Yan Sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ci tura, domin mun gaza samun martaninsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A ‘yan makonnin da suka gabata dai, al’ummar Karamar Hukumar Bukkuyum din na fuskantar yawaitar hare-hare, inda ‘yan bindigar da ake kyautata zaton na boye a dazuzzukan Gando da Barikin Daji ke addabarsu.
Sai dai a harin na ranar Larabar, mazauna garin sun ce ‘yan ta’addar dauke da makamai sun mamaye Birnin Waje ne suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da turmutsitsin mutane da suka ranta a na kare a kokarin neman mafaka.
Hakan ce ta sanya da dama daga ciki suka nufi kwale-kwalen domin tsallaka kogi zuwa garin Zauma, da ke da nisan kilomita 2 daga yammacin kauyen, amma suka nutse.