✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC shiyyar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu mutu wanda motarsu ta fada wani kogi a hanyar Bara zuwa Gombe.…

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC shiyyar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu mutu wanda motarsu ta fada wani kogi a hanyar Bara zuwa Gombe.

Aminiya ta samu cewa masunta ne suka gano wannan mota bayan kwanaki da fadarwarta kogi da ke Tasham Turmi a Karamar Hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.

Kwamandan FRSC reshen jihar Yusuf Abdullahi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi, ya ce an sanar da aukuwar lamarin ne a ofishinsu na Bara kuma nan da nan suka tura jami’ai wurin domin aikin ceto.

Mista Abdullahi ya ce fasinjojin da ke cikin motar duk maza kuma an same su a mace yayin da aka tsamo motar daga cikin kogin.

Ya kara da cewa, an ajiye motar a ofishin ’yan sanda da ke Bara kuma bincike ya kankama domin gano musabbabin aukuwar hatsarin.