Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48.
Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Hotoro.
A cewar Hukumar FRSC, haɗarin ya rutsa da wata motar tirela ƙirar DAF ɗauke da kayayyaki da fasinjoji. Bincike na farko ya nuna cewa direban ya yi tuƙin ganganci saboda gudu wanda hakan ya sa motar ta kauce hanya ta afka ƙarƙashin gadar.
Rahotanni sun nuna cewa, adadin waɗanda haɗarin ya rutsa da su ya kai 71, mutum 48 ne suka jikkata, yayin da 23 suka mutu.
Jami’an bayar da agajin gaggawa na Hukumar FRSC tare da haɗin gwiwar rundunar ’yan sandan Najeriya, sun isa wurin cikin gaggawa domin gudanar da aikin ceto tare da dawo da zirga-zirgar ababen hawa.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed domin kula da lafiyarsu cikin gaggawa.
Bayan faruwar haɗarin, Kwamandan hukumar FRSC reshen Kano, CC UM Matazu, ya tura jami’an bincike domin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin haɗarin.
Ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.