Mutum 145 ne aka sanar da sunayensu a matsayin kwamitin da zai jagoranci shirya bikin auren ’yar Sarkin Bichi, Zahra Nasiru Ado Bayero da angonta kuma dan Shugaban Kasa, Yusuf Buhari.
Kwamitin, wanda Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kafa, shi ne kuma aka dorawa alhakin shirya bikin ba wa sarkin sandar mulki da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje zai yi.
- A karo na 6, an sake tsawaita wa’adin hada layukan waya da lambar NIN
- Jarumai mata 5 da suka taba yin aure kafin shiga Kannywood
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Masarautar Bichi ta fitar, wacce ke dauke da sa hannun kakakinta, Lurwanu Idris Malikawa.
A cewar sanarwar, bikin auren zai gudana ne ranar 20 ga watan Agustan 2020, yayin da shi kuma bikin bayar da sandar zai biyo baya kashegari ranar 21 ga wata a Fadar Sarkin da ke Bichi.
Kazalika, sanarwar ta ce Dagacin Bagwai, kuma Madakin Bichi, Alhaji Nura Ahmad ne zai shugabanci kwamitin, yayin da Falakin Bichi, Alhaji Abba Waziri zai kasance a matsayin Sakatare.
Yayin kaddamar da kwamitin, Sarkin ya sami wakilcin Madakin Bichi, inda ya yi kira ga mambobinsa da su yi amfani da tarin hikimarsu wajen tabbatar da nasarar bukukuwan biyu.