Mutum 14 sun mutu sanadiyyar cin abinci mai guba a ranar Juma’a a kauyen Moda da ke Karamar Hukumar Anka, jihar Zamfara.
Mazauna gidan da suka ci gabar sun shaidawa wakilin Aminiya, cewa wata mata ce ta yi kuskuren zuba sindadarin da ake amfani da shi wajen yin kunshi wanda aka fi sani da “Gishirin lalle”, a cikin miyar don abincin dare wanda ta ce, ta yi tunanin magin Ajino moto.
Duk wanda suka ci abincin sun mutu. Takwas daga cikin wadanda suka mutu sun mutu ne a asibitin da ke makwbtaka da kauyen wanda ke cikin jihar Sakkwato, yayin da shida daga cikin da suka ci abincin suka mutu a gida. Kamar yadda wani da ya bukaci a sakaya sunan shi ya sanar.