Manya da kananan titunan Owerri babban birnin jihar Imo sun kasance babu kowa yayin da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ke ziyarar aiki ta yini guda a jihar.
Kasuwanni da shaguna da makarantu da duk wasu wuraren taruwar jama’a sun kasance a rufe sakamakon umarnin zama a gida da kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra ta bayar ga jama’ar jihar.
Wannan umarni da jama’ar garin ke yi wa biyayya ya zo daidai da ranar da shugban IPOB, Nmandi Kanu yake bayyana a gaban wata kotu a Abuja ne, a inda ake yi masa shari’a.
Shugaba Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Sam Mbakwe da ke Owerri ne da misalin karfe 10:46 na safiyar Talata.
Gwamnan jihar, Hope Uzodinma shi da manyan jami’an gwamnatin jihar ne suka tarbe shi da kuma sarakunan gargajiya na jihar.
Bayan duba wani faretin ban-girma da sojoji suka yi masa, Shugaban ya hau jirgi mai saukar ungulu zuwa kaddamar da titin Owerri zuwa Orlu.
Har ila yau, Buhari ya ziyarci Amaraku inda ya kaddamar da hanyar Owerri zuwa Okigwe, da sabon ginin Majalisar Dokokin jihar da aka yi wa gyara.
Jama’ar garin na zaman gida na tilas ne tun ranar Litinin a cikin biyayyarsu ga haramtacciyar kungiyar ta IPOB.