Mutanen gari sun fasa rumbun Gwamnatin Tarayya a Birnin Ado Ekiti na Jihar Ekiti, inda suka saci takin zamani da irin shuka mai dauke da guba da aka ajiye don rabawa manoma.
Kwamishinan Labarai na jihar, Barista Akin Omole, ya fitar da sanarwar cikin gaggawa domin kaucewa mace-macen da ka iya faruwa bayan mutane sun ci hatsin mai dauke guba.
- An sake saka dokar hana fita a jihar Osun
- #EndSARS: ‘Yan sanda sun hana matasa dibar abincin tallafi
“Bayanan da suka zo mana sun tabbatar da cewa bata-gari sun fasa rumbun gwamnatin tarayya na shirin noma (ADP) da na hukumar bayar da Agaji ta Jiha (SEMA), da sunan satar kayan tallafin COVID-19
“Jihar Ekiti ba ta da wani rumbun da ta ajiye hatsin tallafi COVID-19 saboda duk min rabar da shi kuma abin da mutane suka sata takin zamani ne na NPK da suka yi tsammanin gari ne.
“A cikin rumbun SEMA kuma kayan da za a rabawa wadanda annobar gobara da ambaliyar ruwa ta shafa.
“Wasu sun gudu da irin masara da aka ajiye don a shuka da sauran sinadare da za su yi lahani ga duk wanda ya ci su”.
“Muna rokon mutane da kar su ci abubuwan da suka dauka daga cikin rumbunan saboda za su yi sanadiyar rayuwarsu.
“Jihar Ekiti ba ta da sauran hatsin agaji na COVID-19, duk an rabe su a lokacin kulle” inji kwamishinan.
Wakilin Aminya ya ruwaito cewar mutanen garin sun fita ana ruwa da misalin karfe 7:30 na safe suka rika fasa rumbunan suna kwasar abincin.
An ce daga baya an sanar da sojoji inda suka hana mutane kwasar kayan takin da irin.
Tuni dai mutanen sun fasa rumbun a ranar Jumu’a da niyyar dibar abincin tallafi da Gwamnati ke rabawa domin rage radadin matsin da aka shiga na COVID-19.