Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba gare Shi, muna rokonSa a kowane lokaci muna masu daga hannuwa muna roko cikin kankan da kai gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar ba za ka sama masa wani majibinci mai shiryarwa ba.
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare shi, Mamallaki, kuma Gaskiya Mabayyani. Kuma na shaida shugabanmu, jagoranmu, abin girmamawarmu, mai cetonmu kuma Annabinmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW), mai cika alkawari, amintacce. Allah Ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya don Ya rinjayar da shi a kan duk wani addini. Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a kansa da alayensa tsarkaka da shabbansa jagororin masu jihadi na hannun damansa, yardar Allah ta tabbata a gare su baki daya.
Bayan haka, lallai Allah (TWT) Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kuma kada ku yarda ku mutu face kuna Musulmi. Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba.” (Al-Imrana:102-103). Kuma Ya sake cewa: “Kada ku yi jayayya ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri, lallai Allah Yana tare da masu hakuri.” (Al-Anfal: 46). ’Yan uwana a tafarkin Allah! Lallai duniyarmu tana gudana a bisa wani tsari mai mugun hadari. Ba duniyar Larabawa kadai ba, duk kasashen Musulmi suna fama da wannan bala’i. Muna cikin wani bala’i da aka assasa shi a karkashin wani tsari da ake kira dimokuradiyya. Wannan tafarki har abada ba zai kai mu ga gaci ba, matukar muka bi shi yadda Turawan Yamma suka tsara. Gaskiyar abin da ke akwai babu dimokuradiyya hatta daga wadanda suke riya cewa su ne asalin dimokuradiyyar. Su ne suka assasa ta, kuma su ne masu kira zuwa gare ta, kuma su ne masu kyautata ta. Dimokuradiyya kamar yadda wadannan mutane suke siffanta ta, ba a samunta hatta a Amurka da Birtaniya, kuma ba a samunta har abada a wata kasa ta duniya. Idan hakikanin dimokuradiyya na nufin yin adalci da aiki da shawarwari ne, to, ba za a samu wannan dimokuradiyyar ba, sai a karkashin tsari daya, shi ne tsarin Musulunci. Musulunci ya ba kowane mai hakki hakkinsa, mutum ya samu hakkinsa a karkashin Musulunci, dabbobi ma sun samu hakkinsu a Musulunci. Kowane mai hakki ya samu hakkinsa a Musulunci. A Musulunci kowane mutum na da wani nauyi a kansa. Kowanenku abin tambaya ne a kan kiwon da aka ba shi. Kowane mutum daga cikin Musulmi na da hankali daga Allah da kuma fahimta, kuma abin umarni ne bisa muradin Allah. Kuma Musulmi ne yake kwatanta umarce-umarcen Allah da hane-hanenSa. Kuma kamar ga shi kadai ne aka aiko Manzanni aka saukar masa da littaffai, yana kwatanta aiki da Alkur’ani. Kuma kamar shi kadai ne ake nufi da tsayar da wadannan wajibai, yana imani da Manzon Allah (SAW), kuma a cikin haka yana imani da dukkan Manzanni da Annabawa. Yana karbar umarni daga gare shi (SAW) yana aiki da shi, yana sauraron hane-hanensa yana guje musu. Yana aiki da dukkan wadannan abubuwan da’a da dalilai na shari’a, kai ka ce shi kadai aka umarta da haka. Ba ya taraddadi kuma bai tsayawa ga biyayya ga wadansu, iyaka duk abin da ya ji sai ya bi, saboda sanin cewa wani kebabben al’amari tasirinsa a kan rai ya fi karfi da girma a kan aiki na umumi. Domin idan ka umarci jama’a da wani al’amari su aikata shi, ta yiwu wadansu su yi sakaci su ce wadansu za su yi, su kyale wadansu su yi. Sabanin da za ka umarci mutum ka ce: “Wane yi kaza.” Musulmi mai hankali ba makawa ya sanya rayuwarsa a wannan matsayi. Yana ganin kamar shi kadai aka halitta, ya kasance shi kadai a cikin mahaifiyarsa, aka haife shi, yana rayuwa a wannan duniya a kan kansa shi kadai. Yana ji a jikinsa da tunaninsa cewa shi kadai ne ba wanda yake tarayya da shi a ciki haka. Kuma a barzahu shi kadai ne, sannan a tashe shi, shi kadai, a yi masa hisabi shi kadai, sannan ya yi sa’ada ko ya tabe shi kadai. To idan haka al’amarin yake wajibi ne a kansa ya rika ganin kansa cewa abin tambaya ne a kan komai shi kadai.
Wannan kasa tamu mai mulki da wanda ake mulka, babba da yaro suna shagala da batun zaben wanda zai mulki kasar nan, wanda ya fi cancanta da wanda ya fi dacewa. Wannan idan ma an samu zaben share-fage da zaben gama-gari na gaskiya mai adalci ke nan. Idan kuma ba a samu haka ba, babu abin da zaben zai iya kawowa cikin abin da ake nufi da shi ko ake nufin ya kawo, kuma wannan shi ne abin da ke faruwa a kasashe da dama. Galibi bayan fadin sakamakon zaben akan samu rarrabuwa a tsakanin ’yan Najeriya, wadansu mutane ba su amincewa da sakamakon zaben, yayin da wadansu suka amincewa, me yake kawo haka, an bar ginshiki ko tushe.
Na farko: Imani ingantacce.
Na biyu: Amincewa a tsakanin mutane.
Idan aka samu imani yana hukuta mutum yana tsara tasarrufinsa yana hukunta abin da zai tsayu a kai da abin da zai yi, babu shakka wannan zai haifar da amincewa da shi a zuciyar sauran jama’a, a samu yakini da abin da zai ce, sai a cimma muradi. Sai dai kash, imanin mai rauni ne, an kuma rasa amincewa a tsakanin mutane. Duk lokacin da wani ya ce, sai wani ya kalubalance shi, wannan ne yake jawo tashe-tashen hankula a wurare da dama a wannan kasa da suke haifar da zubar da jini da kashe rayuka da lalata dukiya da korar matasa da dama ko kame su ana sanyawa a kurkuku.
Don haka muna kira ga wadanda alhakin gudanar da al’amura ke hannunsu su dubi gaba kada su duba baya, su dubi makomar kasar nan. Allah Madaukaki Ya sanya wannan kasa ta Musulmi da wadanda ba Musulmi ba da suke watse a sassan kasar nan Kudu da Arewa, Ya nufe mu, mu rayu a haka cikin hikima. Sannan kowane bangare ya rika karfafa mu wajen ci gaba da hidima ga addininmu da hidima ga jama’armu. Ma’ana iradar Allah ta hukunta mu rayu tare, don haka babu makawa mu watsa abubuwan da za su kawo zaman lafiya a tsakaninmu. Bai halatta ga wani bangare a wannan kasa ya tauye wani bangare har ya kai shi ga bango ba.
Ya wajaba mu rayu gaba daya mu riko da addinimu, bai halatta ga waninmu ya ce, tunda wane bai yi adalci ba, ni ma ba zan yi adalci ba, a’a ya wajaba a kan Musulmi ya kasance Musulmi a cikin wahala ko kunci, Musulmi a cikin yalwa ko wadata, Musulmi a lokacin zalunci, Musulmi a lokacin adalci.
Domin haka ne nake kira ga yin adalci. Hakika na fadi a wani taro da aka yi a Kaduna (a shekarun baya), wanda Shugaban kasa na yanzu ya halarta (tsohon Shugaba Goodluck Jonathan), kusan dukkan shugabanni suka halarta kuma malamai masu yawa suka halarta cewa mulki na Allah ne, Yana bayar da shi ga Wanda Ya so. “Ka ce: “Ya Allah Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Kake so, Kana zare mulki daga wanda Kake so, kuma Kana buwayar da wanda Kake so, kuma Kana kaskantar da wanda Kake so, ga hannunKa alheri yake. Lallai ne Kai, a kan kowane abu Mai ikon yi ne.” (k:3:26).
Na ce musu, idan Allah Ya tabbatar da wannan, to, muna karbar kaddararSa da hukuncinSa cikin cikakkiyar yarda. Sai dai a yayin da muke yarda da hukuncinSa, ba zai lizimce mu mu yarda da wadansu abubuwan da suka saba wa abin da muke sa rai ba, ko abin da ya saba wa manufofinmu ba. Kuma a tare da haka wanda yake shugabancin kasar nan ya wajaba a kansa ya kiyaye wadansu al’amura ba tare da lura da kasancewarsa dan Arewa ko dan Kudu ba, Musulmi ko ba Musulmi ba.
Na farko: Ba makawa ya tabbatar da zaman lafiya. Ba makawa ya himmantu ga batun zaman lafiyar kasar nan da aminci ga addini da samar da aminci ga rayuka da aminci ga hankula da aminci ga nasaba da aminci ga dukiya da aminci ga muhallin da mutane suke rayuwa.
Na biyu: Babu makawa wajen tabbatar da adalci mudalaki a tsakanin dukkan mutanen kasar nan. Adalci shi ne gishiki ga kowane mai mulki. Idan babu adalci ba za a samu zaman lafiya ba, ba za a samu ci gaba da bunkasa ko daukaka kasa ba.
Na uku: Muka ce babu makawa a rika samun daidaito a tsakanin mutane a cikin mu’amala da hakkoki. Wannan kasa Allah Madaukaki Ya ba ta albarkatu masu yawa da za su iya biyan bukatun daukacin al’ummarta. Amma muna ganin yadda kasar nan take fama da wahalar rashin ruwa da wutar lantarki da karancin magunguna da tabarbarewar ilimi da karancin komai har zuwa mafi karancin abin da dan Adam yake bukata na yau da kullum.
Ba wai muna bukatar motocin shiga na alfarma ko jiragen sama ko kumbo ba ne. A’a muna bukatar abin da dan Adam ke bukata ne don ya rayu.
Na hudu: Sa’annan na ce: Wannan kasa-dukkanmu- muna ganin abubuwan da suka wajaba a kanmu mu guje su, barnar da ta fi su, ita ce almundahana sai barnar siyasa da barnar masu mulki da fasadin zamantakewa da barnar a fagen tattalin arziki, har ta kai mu ga fasadi da barna sun shafi kowane bangare na hukunci. Domin haka babu shakka kowane Musulmi ko kowane mutum mai hankali a wannan kasa ya gano cewa bangarori uku da suke tafiyar da mulkin kasar nan bangaren shari’a da na majalisa da na zartarwa dukkansu wadanan masu fasadi ke juya su. Wadannan masu fasadi ba su ne dukkan mutanen kasa ba, a’a wadansu ’yan kalilan din jama’a ne sanannu, amma suna ta watsa fasadi a cikin kasa.
Domin haka duk wanda yake ko zai mulki kasar nan, idan yana son samar da cikakkiyar zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasa, kuma idan yana son ya yi amfani da mulkinsa a wannan kasa wajen samun yardar jama’a, to wajibi ne a kansa ya bi wadannan hanyoyi, kuma ya yi aiki sosai domin yin gyara.
Musulunci ya fi dimokuradiyya ba jama’a hakkinsu (1)
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba gare Shi, muna rokonSa a kowane lokaci muna masu…