Fassarar Salihu Makera
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin annabawa, Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya shiryar da mu ga wannan, ba za mu shiryu ba, ba domin Allah Ya shiryar da mu ba. Hakika manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya.
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai Shugabanmu kuma masoyinmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, Allah Ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi a kan kowane addini koda kafirai ba sa so. Ya Ubangiji! Ubangijin aminci, Ka yi aminci a kan sirrin aminci a cikin sirrin aminci da sirrin aminci da salama. Ka yi taslimi a kan hasken aminci a cikin hasken aminci da hasken aminci, salati da taslimi da’immanmu masu lizimta juna matukar mulkin Allah aminci ne. Ya Mai aminci, Ka yi sallama da aminci da zaman lafiya a cikin aminci, muna neman aminci daga gare Ka, ya Mai aminci. amin.
Bayin Allah! Ku bi Allah da takawa, ku Musulmi saboda Musuluncin da sirrin aminci da salama da zaman lafiya ya zo mana da shi, wato Annabi Muhammad bin Abdullahi, wanda aka aiko shi a matsayin rahama ga dukan halitta ya zo da adddinin aminci da salama da zaman lafiya.
Addinin da Allah Ya zabe shi domin bayinSa, kuma Ya yardar musu shi, Ya dora su a kansa, shi ne Musulunci ba wani ba. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne addini a wurin Allah shi ne Musulunci.” Kuma Madaukaki Ya ce: “Wanda ya bi wanin Musulunci a matsayin addini, ba za a a karba daga gare shi ba, kuma shi a Lahira yana daga cikin masu hasara.”
Don haka babu wani Annabi ko Manzo face yana bin wannan addini, kuma yana mai sallama kansa ga Allah Ubangijin halittu. Kuma ya umarci al’ummarsa da haka. Alkur’ani mai bayar da labari da shaida ne a kan haka. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma a lokacin da Ibrahim yake daukaka harsashin gini ga dakin da Isma’ila (suna cewa): “Ya Ubangijinmu! Ka karba daga gare mu, lallai ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani. Ya Ubangijinmu! Ka sanya mu, mu biyu wadanda suka sallama (al’amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al’umma mai sallamawa zuwa gare Ka, kuma Ka nuna mana wuraren ibadar hajjinmu, kuma Ka karbi tuba a kanmu. Lallai ne Kai, Kai ne Mai karbar tuba, Mai rahama. Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo daga gare su, yana karanta ayoyinKa, kuma yana karantar da su Littafin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lallai ne Kai, Kai ne Mabuwayi Mai hikima. Kuma wane ne yake gudu daga akidar Ibrahim, face wanda ya jahilta ga ransa? Kuma lallai ne, hakika, Mun zabe shi a cikin duniya, kuma lallai ne shi, a cikin Lahira yana daga salihai. A lokacin da Ubangijinsa Ya ce masa: “Ka sallama,” ya ce: “Na sallama ga Ubangijin talikai. Kuma Ibrahim ya yi wasiyya da ita ga ’ya’yansa, kuma Ya’akubu (ya yi wasiyya, suka ce): “Ya ’yayana! Lallai ne, Allah Ya zaba muku addini, don haka kada ku mutu face kuna Musulmi.” (k:2:127-132).
Wanda sha’aninSa ya girmama ya ce game da Annabi Lud (AS) game da al’ummarsa cewa: “Ka fitar da mu wanda ya kasance daga cikin muminai. Ba Mu samu a cikinta ba wani gida na Musulmi.”
Ya bayin Allah! Allah Madaukaki bai gushe ba,Yana yi mana magana a kan Musulunci a jiya, Musulunci addini ne na wadanda suka gabace mu na daga annabawa da manzanni, domin wadanda suke da sani su samu yakini, wadanda ba su da sani sa sani cewa lallai Musulunci dukansa aminci ne da zaman lafiya. Kuma Allah ba zai gaji kasa da abin da ke kanta ba, face da guguwar taimakon aminci da zaman lafiya da tutocinsa. Allah Madaukaki Ya ce a kan Hawariyyuna mabiya Annabi Isa dan Maryam (AS): “To a lokacin da Isa ya gane kafirci daga gare su, sai ya ce: “Su wane ne mataimakana zuwa ga Allah?” Hawariyawa suka ce: “Mu ne mataimakan Allah. Mun yi imani da Allah. Kuma ka shaida cewa, lallai ne mu, masu sallamawa ne, (Musulmi). Kuma Madaukaki Ya ce: a cikin Suratu Shura: “Ya shar’anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nuhu da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrahim da Musa da Isa cewa ku tsayar da addini sosai, kuma kada ku rarrabu a cikinsa.” (k:42:13). Kowane annabi daga cikin annabawa ya zo ne da aminci da sallamawa wato Musulunci da amintar da Musulmi. Kuma Allah Ya aiko kowane manzo ne daga cikin manzanni da aminci ga duniya ta hanyar Musulunci. Ba za a samu aminci da zaman lafiya ba, sai tare da Musulunci ta hanyar fahimtarsa da tsarkake ibada ga Allah Madaukaki.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ka tsayar da fuskarka ga addini tsarkakakke, fidirar Allah wadda Ya dora mutane a kanta, babu musaya ga halittar Allah. Wannan shi ne addini madaidaici, sai dai mafi yawan mutane ba su sani.”
Mai tsira da amincin Allah yana cewa: “Lallai wannan addini sauki, duk wanda ya tsananta zai gallabe shi.” Ku saukaka ya ku bayin Allah game da addininku! Kada ku tsananta, domin a tare da tsanani akwai wani sauki. Kuma a tare da tsanani akwai wani sauki. Idan ka gama ka kafu. Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwadayi. Wala haula wala kuwwata illah billahil aliyyil azim.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Wanda Ya aiko ManzonSa a matsayin rahama ga dukan halittu, kuma Ya ce: “RahamaTa ta yalwaci komai.” Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Mai rahama, Mai jin kai. Kuma na shaida lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammad ManzonSa ne zuwa ga dukan mutane yana mai bushara da gargadi, kuma shi ne mai tausayi ne mai jin kai.
Ya bayin Allah! Musulunci addini ne da daula, shi ne addinin da mabiya Annabi Muhammad kuma shi ne addinin kowane zamani. Duk wani addini da ya saba da hanyar Annabi Muhammad shi bata ne kuma batacce ne. Kuma ba ya ga haka, shi daula ne abari yabo da godiya. Duk daular da ta saba da wannan ita hasara ce da tabewa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kirkiro a cikin wannan al’amari namu wanda ba ya cikinsa, to an mayar masa.” Allah Madaukaki Ya ce: “Wadanda suke saba wa al’amarinsa (umarninsa SAW), su ji tsoron wata fitina ta same su, ko wata azaba mai radadi ta shafe su.”
Don haka zaman lafiyar duniya yana hannun Allah, sa’annan yana hannunmu gaba daya. Allah Yana nufinmu da sauki ne ba Ya nufinmu da tsanani. Ya ce: “Magana c eta aminci daga Ubangiji Mai jin kai.” Kuma Ya ce: “Shi aminci ne har zuwa bullowar alfijir.” Ya ce: “Aminci ya tabbata ga Nuhu a cikin talikai.” Kuma Ya ce: “Aminci ya tabbata gare ku, kuna masu jin dadi, don haka ku shige ta (Aljanna) kuna masu dauwama.” Kuma Ya ce: “Muka ce: “Ya ke wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahim.” Kuma Ya ce: “Aminci ya tabbata a kan manzanni. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.”
Daga cikin sunayen Allah masu kyau akwai Assalamu (Mai aminci), don haka Muslunci addini ne na aminci daga Ubangijin aminci ta hannun Manzon aminci.
Idan ya kasance sakon Annabi (SAW) sako ne umumi, to duk wanda yake cikin duniya a yau yana daga cikin wadanda aka aiko Manzon Allah (SAW) zuwa gare shi, to yaya za mu sadar da wannan aminci ba tare da Musulunci ba?
Aminci wata manufa ce da ake cin masa bisa taimakon Ubangijin amincin da sallamawar Musulmi sallamawa ta gaba daya ga Ubangijin talikai. Wannan shi ne abin da zai ja mu ko ya kusantar da mu zuwa ga cimma manufa ta tabbatar da aminci a duniya. Kuma domin a samu amana akwai bukatar a kiyaye abubuwa masu zuwa:
1.Neman ilimi da fahimtar addini.
2.Aiki da ilimin da yada shi.
3.Takawa.
4.Yakar zuciya ta bi abin da Allah Yake so.
5.Kira zuwa ga gaskiya.
6.Kyawawan dabi’u da halaye.
7.Cikakkiyar biyayya ga Manzon Allah (SAW).
8.Nuna sanyin hali da guje wa ayyukan kazanta.
9.Guje wa munafunci da munafukai
10.Hadin kai da son juna.
11.kaurace wa ta’assubanci da kabilanci.
12.Kyautata niyya da kyautata zato ga juna.
13.Yawaita addu’a.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya kasance ana aiko kowane annabi ne zuwa ga al’ummara su kadai, amma ni an aiko ne zuwa ga dukan al’umma farare da bakake.”
Allah Madaukaki Ya ce: “Allah Yana kira zuwa ga gidan aminci kuma Yana shiryar da wanda Ya so zuwa tafarki madaidaici. Ga wadanda suka kyautata suna da sakamakon kyautatawa da kuma kari.”
“Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci, Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.” Don haka ku tuna Allah Mai girma da daukaka, sai Ya tuna da ku, kuma ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku. Kuma ambaton Allah ne mafi girma. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa.”
Za a iya samun Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan, ta tarho: 080347108620