✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci da neman halal (2)

Fassarar Salihu Makera Daga nan za mu fahimci girman wannan addini da falalarsa da kusancin Musulmi mumini ga Allah Madaukaki da kuma cewa lallai Manzon…

Fassarar Salihu Makera

Daga nan za mu fahimci girman wannan addini da falalarsa da kusancin Musulmi mumini ga Allah Madaukaki da kuma cewa lallai Manzon Allah (SAW da aka ce rahama ne shi. “Kuma ba Mu aiko ka ba face rahama ga talikai. (Al-Anbiya’i: 107), hakika rahama din ne ga dukkan halittu kamar yadda Allah Madaukaki Ya fada. Kowane lokaci yana tafiyar da mu cikin kwadayin alheri bisa karfi ko gazawarmu, wannan ne ya sa Allah Madaukaki Ya zabe shi da kyawawan halaye da dabi’u masu girma. Sai Allah Ya ce: “Lallai ne kai kana a kan halayen kwarai masu girma.” (Alkalam:4).

Allah Ya yi mana albarka ni da ku a cikin Alkur’ani Mai girma, kuma Ya shiryar da ni da ku da abin da yake cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima. Lallai Shi Madaukaki Mai yawan kyauta ne Mai karimci, Mamallaki Mai tausayi, Mai jinkai.

 

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, godiyar da take mukarana da hikimar Allah cikakkiya, yana kewaye da ni’imarSa mai yawa, kuma Ya kebe ni’imarSa a kanmu da imani da Musulunci, kuma lallai ita ce mafi girman ni’ima. Muna gode maSa Madaukaki Mai girman daraja da Ya sanya mu daga cikin al’ummar shugabanmu Muhammad (SAW) wadda ita ce mafificiyar al’umma.

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin  tarayya a zatinSa da siffofinSa, shaidawar da take barranta daga shirka da shakka da zunubi. Kuma na shaida lallai shugabanmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa (SAW) wanda ya siffantu da dukkan halaye ababen godiya da dabi’u masu girma, kuma  ya kebanta da cikakkiyar kusanci da gabata.

Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci a bisa shugabanmu Muhammad mai shriyarwa zuwa ga tafarki madaidaici da alayensa da sahabbansa ma’abuta yarda da sallamawa.

Bayan haka,  ya ku ’yan uwa! Manzon Allah (SAW) ya lura cewa wani mutum daga cikin sahabbansa duk lokacin da ya yi Sallah ba ya zama sai ya fice daga masallaci cikin gaggawa zuwa gidansa. Kuma irin wannan aiki a zamanin Manzon Allah (SAW) ba a san shi ba, sai a cikin mutanen da ayyukansu suka wofinta daga imani, su ne munafukai. Munafukai ba sa zama bayan idar da Sallah, suna ficewa daga masallaci kamar ana korarsu daga ciki. Sai (SAW) ya yi tambaya game da shi, sai aka ce ai wane ne. To yayin da (SAW) yake zaune a cikin sahabbansa sai wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) yana tambayarsa wani abu daga dukiya. Sai (SAW) ya ce: “Shin ba ka da komai ne a gidanka?” Sai ya ce: “Eh ina da bargo da muke rufuwa kuma muke shimfida rabinsa. Ma’ana muna rufa da rabinsa muna shimfida rabinsa. Sai kuma kwarya. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka zo min da su.”

Ku duba Manzon Allah (SAW) yana koya mana ibada yana koya mana ada yana koya mana yadda za mu kyautata da yadda za mu gyara mu inganta Lahirarmu. Yana koya mana yadda za mu kyautata zamantakewarmu a wannan duniya. Ka zo min da su ka zo min da bargon da kwaryar. Sai ya zo masa da su. Sai Manzon Allah (SAW) ya rike su a hannunsa ya ce: “Wane ne zai sayi wadannan daga gare ni?” sai wani mutum ya tashi ya ce: “Ya Manzon Allah! Na saye su Dirhami daya.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wane ne zai yi kari? Sai biyu ko su uku. Sai wani mutum ya mike ya ce: “Ya Manzon Allah! Na saye su Dirhami biyu.” Sai ya ce: “Kawo su.” Ya karbi Dirhami biyun ya mika wa mutumin ya ce da mai rokon (Wani mutum ne daga Ansar): “Zo ka karbi Dirhami biyun, ka sayi abinci da daya ka kai wa iyalinka, ka sayo gatari da daya ka kawo min.” Sai ya je ya sayo gatarin bayan ya sayi abinci ya kai wa matarsa. Sai (SAW) ya ce: “Ku kawo min kota ko ya nemo kota ya sanya gatarin a cikinsa ya ce masa “Ka tafi kada in sake ganinka sai bayan kwana goma sha biyar… ka yiwo itace ka sayar kada in gan ka.” Sai mutumin ya tafi ya shafe kwana goma sha biyar yana itace yana sayarwa.

Ku dubi yadda ciyar da iyali da yin aiki don haka domin kauce wa rokon mutane ke da kima. Ku dubi wajibcinsa a kan mutane har ya rinjaya a kan wasu ayyukan ibada masu girma. Wannan mutum Manzon Allah (SAW) ya umarce shi ya bace na Juma’a biyu kada ya halarci Sallar Juma’a, yana aiki don me? Yana aiki har wa yau don addininsa, koda hakan ya zamo al’ada wannan al’ada (ta ciyar da iyali da rashin roko) ta zama ibada.

Sai mutumin ya tafi bayan mako biyu ya zo ga Manzon Allah (SAW) ya mallaki Dirhami goma- Allahu Akbar!- Dirhami goma!! Ya saya wa kansa tufafi, ya saya wa matarsa, ya saya musu abinci. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce da shi: “Wannan ya fiye maka alheri da a ce ka zo Ranar Kiyama rokon mutane ta jawo maka baki a fuksa Ranar Kiyama.” Ma’ana wannan aiki naka zai kubutar da kai daga ka zo Ranar Kiyama da alama baka a fuskarka saboda rokon mutane. A wata ruwayar: “Wannan ya fiye maka alheri daga ka roki mutane su ba ka ko su hana ka.”

A karshen nafsin wannan Hadisi Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa roko ko bara ba sa halatta sai a cikin abubuwa uku: Ga ma’abucin tsananin talauci, wato ga fakirin da bai mallaki komai ba sai turbayar da yake zaune a kanta, to irin wannan mutum ya halatta ya yi roko ko bara ya nemi abincinsa da na iyalinsa. Na biyu wanda bashi ya yi masa katutu ko kuma ya yi lamuni ga wani ya kasa biya. Shi ne mutumin da bashin ya yi masa yawa har mutane suke cewa bashi ya yi wa wane daurin gwarmai, to wannan ma ya halatta ya yi roko ko bara ga kansa ko waninsa.

Na uku shi ne wanda diyya ta hau kansa. Misali daya daga cikin danginsa ya kashe wani bisa kuskure aka ce ya biya diyya, sai aka dora musu biyan diyya to ya halatta ya yi roko ko bara kuma jama’a su taimaka masa har ya biya wannan diyya.

Don haka roko ko bara ba sa halatta sai ga wadannan mutum uku, mai tsananin talauci ko wanda bashi ya yi masa kanta ko wanda biyan diyyar jini ya hau kansa kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce.

Manzon Allah (SAW) ya shirya mu ya koyar da mu cewa a cikin kowanne daga cikin wadannan abubuwa ya wajaba a kanmu mu nemi taimakon Allah. Ya wajaba a kanmu mu koma ga Allah. Duk abin da ya samu dan Adam na kunci da tsanani ko masifa ko annoba… ya wajaba a kansa ya mika wannan zuwa ga Allah Madaukaki. Kan haka ne ya zo a cikin wasu hadisai cewa wanda yunwa ko bukata suka shafe shi ya kai kuka ga mutane sai Allah Ya buda masa kofar talauci marar karewa. Idan kuma ya mika lamarin ga Allah, sai Ya isar masa Ya azurta shi ta inda ba ya zato. Don haka kada mu yi nesa da Allah, mu tabbatar kullum muna kusantar Allah Madaukaki.

Sannan Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi mana algushu ba ya tare da mu.” Don haka ya wajaba a kanka ya kai dan kasuwa da kai ma’aikaci da kai mai sana’a da kai manomi da kai malami da kai mai wa’azi da kai mai koyarwa da kai mai nusarwa, ka lizimci yin nasiha (kyautatawa da saukakawa) domin nisiha ita ce addini gaba daya.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Addini nasiha ne. Muka ce ga wa ya Manzon Allah? Ya ce: “Ga Allah da LittafinSa da ManzonSa da shugabannin Musulmi da talakawansu.”

Don haka ya wajaba a kan Musulmi ya yi nasiha a cikin komai da duk aikin da Allah Ya ba ka. Na shaida lallai Allah ne Ya ba ka wannan aiki da kake yi, don haka ya zamo zuciyarka tana ta’allake da Allah. Kada ka rika tunanin wani abu daban, kada ka dogara a kan wayonka da karfinka da dabararka. Ba ka san abin da ya wuce ba, ba ka san halin da kake ciki ba, kuma ba ka san abin da zai zo ba. Dukkan wadannan iliminsu yana wurin Allah ne. Za ka iya wayar gari ba ka samu wani mala’ika a cikin sama ko mutum a kasa ya san abin da Allah zai aikata a cikinta ba. Ya kebanta Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a ilimin abin da zai faru a wannan duniya.

Don haka mafi alheri ka lizimci yin nasiha kuma ka tsaya a kofar Allah wajen yin addu’a da kankan da kai har Allah Madaukaki Ya kwaranye abin da ke damunka. Kuma kada ka manta cewa an umarce ka da bin Manzon Allah (SAW) a cikin komai. “Idan kuka yi masa da’a sai ku shiryu.” (Nur:54).

Ya bayin Allah! Lallai Allah Madaukaki Ya umarce ku da wani al’amari da Ya fara da kanSa, kuma Ya yabi mala’iku masu tasbihi a kansa, Ya ukunkta ku da shi ya ku muminai na daga aljanu da mutane, sai Ya ce: “Lallai Allah da mala’ikunSa suna salati a kan Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi da taslimi da sallamawa.” (Ahzabi: 56).

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi mini salati daya, Allah zai yi masa salati goma madadinta.”

Allahumma salli wa sallim wa barik ala sayyidina Muhammad sahibil Haudil maurud, almukamu fil mukamil Mahmud, wala alihi zawil fadlil jalliy, wa as’habihi zawil kadril aliy, Abi Bakrin wa Umar wa Usman wa Aliyyu. Wa’ardil lahumma an as’habin nabiyyika ajma’in wa anit tabi’ina wat tabi’it tabi’ina wa man tabi’ahum bi ihsani ila yaumid dini. Wa anna ma’ahum bi rahmatika ya arhamur rahimin.