Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce addinin Musulunci bai haramta wa malamai shiga motoci masu tsada da gidaje na alfarma ba:
Me za ka ce game da shawarar da Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bai wa malamai cewa su rika gudanar da rayuwa mai sauki domin su zama abin koyi, maimakon rungumar abin duniya na shiga motoci masu tsada da gidaje na alfarma da sauransu?
Gaskiya ni abin da nake gani kan wannan nasiha ko shawara da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bai wa malamai shawara ce mai kyau ga al’ummar Musulmi baki daya domin addinin Musulunci addinin ilimi ne. Don haka Allah ya bude Alkur’ani Mai girma da cewa “Ka yi karatu da sunan Ubangijinka Wanda Ya yi halitta.” Kuma ilimin da ake nufi a tsarin addinin Musulunci shi ne ilimin shari’ar Allah, wanda Ya aiko Annabi Muhammad (SAW) da shi a cikin Alkur’ani Mai girma. Kuma Allah Ya umarci Annabi Muhammad (SAW) ya fassara nassoshin da ke cikin cikin Alkur’anin. Ka ga duk abin da za a fada a ce ya dace ko bai dace ba. Mu al’ummar Musulmi ba da ra’ayi za mu yi aiki ba da Alkur’ani za mu yi aiki domin nan ne daidai.
Sannan babu mai fassara Alkur’ani kamar Annabi Muhammad (SAW) wanda ya yi wa duniya fassarar Alkur’ani kamar yadda Allah Ya umarci ya yi. Malami zai yi rayuwa mai daraja ya zauna a wuri mai kyau ya samu abinci mai kyau ya auri mace mai kyan hali da tsabta da kyakkyawar magana da lura da mutumcinsa da mutumcin makwabtansa.
Maganar yin haka ta fito ne daga Alkur’ani Mai girma don kawar da barnar sufaye masu cusa wa Musulmi ya zama koma-baya, inda suke cewa wai malami ya zamanto kazami, ba ya noma ba ya kiwo har aka samu muguwar karin maganar da ake cewa tsammanin warabuka Malam ya ki noma domin zakka.
Har wadansu suna cewa malamai sai na da, domin wai malamai na da, suna zama a daki ne idan aka saukar da ruwan damina sai su turo da kafarsu daga waje, sai su ce Allah Ya kawo mu. Ka ga a wannan darasi malami ba ya komai ke nan, wanda ya saba da malinta irin ta Sayyadina Abubakar ke nan, domin shi dan kasuwa ne kuma attajiri ne. Malami ba ya noma ba ya kiwo, ba irin rayuwarsu su Sayyidina Usman Bin Affan ba ne, wanda yana cikin masu dukiya na sahabbai. Wanda idan za a fita wajen jihadi yana dibar dukiyarsa ya bayar don daga addinin addinin Musulunci. Annabi Muhammad (SAW) da sahabbai su hau managartar dawaki su rike ingantattun makamai don kare addinin Allah.
Idan wani ya zo ya ce malami ba ruwansa da daddadan abubuwa, babu ruwansa da yalwatatcen gida babu ruwansa da abin hawa mai kyau. Sai mu ce bari mu duba Alkur’ani mu ga me Allah Ya ce. Idan wadansu suna cewa malami ko Musulmi zaman nakasu zai yi, kada ya ci mai kyau kada ya sha mai kyau kada ya hau abin hawa mai nagarta kada ya yi ado, a Alkur’ani sai Allah Ya ce Annabi (SAW) ya tambayi duniya duk wane ne Ya haramta ado na Allah? Wannan kayan adon da Allah Ya fitar da su a duniya don bayinsa managarta ne.
Sai Allah Ya ba da amsa ya ce ya Annabi Muhammad (SAW) ka ce kayan ado da dadadan abinci Allah Ya halatta su ne kuma Ya fitar da su ne ga wadanda suka yi imani da Alkur’ani da Hadisi da koyarwa Annabi (SAW). Don haka duk kayan adon da ka ga ni a duniya, Allah Ya yi su don masu imani wato malaman addini masu imani kayan ado nasu ne dadadan abincin nasu ne, inji Allah.
Idan ka ga kafiri da kayan ado ya ci arzikin Musulmi ne ba don shi Allah Ya yi ba, idan ka ga fasiki ko munafiki ko kafiri da kayan ado da dadadan abinci ya ci arzikin Musulmi mai imani ne.
Har ila yau Allah Ya ce kayan ado na Aljanna da dadadan abinci na Aljanna da kyawawan abin hawa na Aljanna na masu imani ne malaman nan na addinin Musulunci, masu aiki da addini. Wadanda ba sa shiga cikin harkallar cin kamama tare da azzalumai. A Lahira ban da fasikai da munafukai, domin a duniya ne fasiki da munafuki suke cin arzikin Musulmi mai imani.
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce yana daga arzikin mutum Musulmi ya samu managarciyar mace ya aura da gida fankameme maganarci. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce daga cikin arziki ga mutum ya samu abin hawa mai kyau gangariya. Kuma malami mai karantar da jama’a kada ya karantar da jama’a cewa koma bayan duniya su ne malamai, sai wani ya dinka riga ya sanya
ta datse ya sanya a yi mata faci, ya dauka ya bai wa malami. Idan mutum ya yi haka ya wulakantar da ilimi, domin Annabi (SAW) bai dora mu a kan wulakanta malamai ba, ya ce mana buwaya ta Allah ce buwaya ta Manzon Allah ce da muminai.
Kuma Manzon Allah ya gaya mana cewa siyasar duniya gaba daya, tun farkon zamani wato zamani su Annabi Haruna da Annabi Musa (AS) masu jagorancin siyasarsu Annabawansu ne. Kuma malamai magada Annabawa ne, ka ga a jefa wa wasu Musulmi rauni su zama kazamai ko raunana, a ce kada su hau abin hawa mai kyau. Su bar wa kafirai da mufukai da fasikai kayansu da siyasarsu ya saba wa shari’a.
A darasin Musulunci a duk bangarorin rayuwa ba a yarda Musulmi ya yi rauni a kai ba, Allah Ya ba mu darasi mai albarka a Najeriya don haka na gaskata shawarar da Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bai wa malamai. Domin kana duban Mai alfarma Sarkin Musulmi ka san daga gidan malami ya fito shi ne Shehu Usman dan Fodiyo, idan ka je ka dubi gidan Sarkin Musulmi za ka ga cewa ya fito daga gidan malami ne. Kana ganin Sarkin Kano za ka ga daga gidan malami ya fito, kana ganin Sarkin Katsina za ka ga daga gidan malami ya fito. Dukan wadannan manyan sarakuna daga gidan malamai suka fito, dukan wadannan sarakuna idan ka ga ba sa yin wa’azi sun sanya wadansu suna yi musu ne. Amma aikin malantar nasu ne domin sun fito daga gidajen malamai ne, don haka babu nakasu a wurin malami.
Wato a Musulunci ba laifi ba ne malami su rika shiga manyan motoci masu tsada da manyan gidaje masu kyau?
A Musulunci bai laifi b ane domin Allah Ya ce duk kayan adon da ka ga ni a duniya, Allah Ya yi su don masu imani wato malaman addini masu imani, kayan ado nasu ne dadadan abincin nasu ne inji Allah.
Kuma abin da nake ganin manufar Mai alfarma Sarkin Musulmi yake nufi shi ne, kada malami ya shiga cikin ’yan duniya a raba kudin makamai da shi, idan za a cuci kasa kada a samu malami a ciki, idan za a yi kade-kade da raye-raye kada a samu malami a ciki, idan za a yi dukan wasu miyagun ayyuka kada a samu malami a ciki.
To a karshe wane sako ne kake da shi zuwa ga malamai?
To lallai ne malamai su kama kansu su yi rayuwar da za a yi koyi da ita, su dora jama’a a kan gaskiya da rikon amana da cika alkawari. Kada a samu hanun malami wajen sace kudaden jama’a. Malamai su wadatu da abin da Allah Ya ba su na halal, malamai su nemi halal su ci mai kyau su sha mai kyau, su samu motoci masu kyau su auri mata nagartattu masu kyau, domin Allah Ya hallata musu.