✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

MUSHA DARIYA: Bahadeje da Banufe

Wani Banufe ne da wani Bahadeje  na rokon Allah a Dakin Ka’aba. Sai Banufen ya ji Bahadejen da ke kusa da shi ya daga hannu…

Wani Banufe ne da wani Bahadeje  na rokon Allah a Dakin Ka’aba.

Sai Banufen ya ji Bahadejen da ke kusa da shi ya daga hannu yana cewa: “Ya Allah! Duk abin da Ka ba Banufen nan, ka ba ni ninkinsa biyu.”

Ko da Banufen nan ya ji haka, sai ya ce: “Ya Allah! Ka sa idona daya ya nakasa.”

Wato idan idon Banufe ya mutu, shi Bahadeje zai rasa nasa idanun biyu duka.

 Daga Kabir Sakaina Layin ’Yangoro, Malumfashi