An shawarci masu sana’ar sayar da shayi da biredi da su yi rajista da kungiyar masu sana’ar don taimakon juna, kawar da baragurbi da kuma bunkasa sana’ar don a gudu tare a tsira tare.
Shugaban kungiyar masu sana’ar sayar da shayi da biredi na yankin Kudancin Kaduna Mika’il Jibril da aka fi sani da Miko Maishayi da ke garin Kafanchan (karkashin kungiyar TABSAN ta Jihar Kaduna) ne ya bayyana haka ga Aminiya yayin wata tattaunawa.
Miko, ya bayyana cewa ko a yau mutum ya bude shagon sayar da shayi da biredi to washegari za su kai masa ziyara tare da tallata masa kungiyar don yin rajista kuma kafin rajistar, sai an tantance daga inda mutum ya fito domin tsaftace harkar daga masu fakewa da ita
alhali suna bude shagon ne don zama wata mafaka na kulle-kullen miyagun ayyuka.
“A yanzu da muke kan tantance masu wannan sana’ar, mun sami mutum 139 da su kayi rajista da mu. Ka san duk abin da ake yi a kungiyance ya fi amfani domin ko gwamnati ce za ta taimaka tana duba mutane ne a kungiyance ba daidaiku ba. A yanzu haka ma akwai kayayyakin da
kamfanin madarar Peak su ka kawo mana saboda lura da irin taimakonsu da masu sayar da shayi ke yi kuma nan gaba ma kamfanonin Nescafe da na Indomie da Bournbita da sauransu za su hada kai damu domin sun kura babu inda su ka fi samun ciniki sai ta hanyar masu sayar da shayi da biredi domin kayan shayi sai ya yi watanni a shaguna ba a saida ba amma da zaran sun shigo shagon shayi sai a saye su nan da nan.” In ji shi
Sannan ya bayyana cewa ko a kwanakin baya shugabannin kungiyarsu ta jiha sun kawo musu ziyarar karfafawa. Shugaban ya kuma bayyana cewa daga cikin ayyukan kungiyarsu akwai
taimakawa juna idan wani ya shiga wani hali da sauransu, don haka ya yi kira ga shugabanni da su taimakawa irin wannan kungiya mai matukar amfani a cikin al’umma.