✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna neman tallafi daga gwamnati – Alhaji danladi

Wani dan kasuwa da ke sayar da kayan tireda da kayayyaki irin na fulani a babbar kasuwar Muda Lawan da ke Jihar Bauchi ya bayyana…

Wani dan kasuwa da ke sayar da kayan tireda da kayayyaki irin na fulani a babbar kasuwar Muda Lawan da ke Jihar Bauchi ya bayyana cewa babbar matsalar ’yan kasuwar Arewa-maso-Gabas suke fuskanta ita ce ta rashin jari.
dan kasuwar mai suna, Alhaji danladi ya ce ’yan kasuwan yankin sun dauki tsawon shekaru shida suna fama da tashe-tashen hankula wanda ya yi sanadiyyar lakume dimbin rayuwar al’umma.
Ya kara da cewa “tun lokacin da aka rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun bana muka fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kowa ya ga yadda hukumomin tsaro suke aiki ba dare ba rana domin murkushe masu ta da kayar baya,” inji shi.
Daga nan ya yi kira da jihohin Barno da Yobe da Adamawa da Gombe da Taraba da kuma Bauchi da su tallafa wa ’yan kasuwa da jari “domin da yawa daga cikin ’yan kasuwa sun cinye jarinsu sakamakon matsalar tsaro da ta addabi yankin a shekarun nan.”