Yayin da ake cikin mako na biyu da kai farmaki a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta ’Yan mata da ke garin Dapchi a Jihar Yobe, tashin hankali da jimamin da iyaye da al’ummar gari da gwamnatocin jiha da na tarayya suke ciki sai kara hauhawa yake yi.
A farfajiya makarantar, musamman inda yaran suke zaune, a ranar farmakin domin yin buda bakin azumin da suka saba da shi na ranar Litinin, awaki ne kadai ke tsintar burbushin abincin da yaran suka zubar domin guje wa shiga tarkon ’yan ta’addar.
Hakan ya bar iyaye da sauran ma’aikatan makarantar cikin matukar juyayi kan yadda rayuwar yaran za ta kasance sakamakon rashin yin buda baki da kuma bala’in da za su tarar da shi a hannun ’yan Boko Haram na daga rashin abinci da fargaba.
Daga cikin mutanen da Aminiya ta tattauna da su, wadansu daga cikin iyayen daliban sun ce a gaban idonsu mayakan Boko Haram din suka shiga garinda misalin karfe 6:30 inda suka bata kimanin awa daya a cikin makarantar kafin suka bar garin.
A gabana aka sace mana ’ya’ya – Ibrahim Nasiru
daya daga cikin iyayen yaran Malam Ibrahim Nasiru ya bayyana wa Aminiya cewa a gabansa aka sace musu ’ya’ya amma ba su da yadda za su yi saboda ba su samu wani dauki daga jami’an tsaro ba.
Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce suna zaune goshin Sallar Magriba, sai suka ga jerin motoci kirar Hilud guda 12 da babura kirar Kasiya sun bullo daga gabashin garin Dapchi, wadanda suka dauka sojojin gwamnati ne saboda fentin motocin da kakin da suke sanye da shi irin na soji ne. Ya ce isowarsu ke da wuya sai suka fara harbi wanda hakan ya sa mutanen garin suka tsorata, kowa ya nemi mafaka sai suka fara cewa “Sarino! Sarino! Sarino! Sario-ayimadiyewa,” wato ku je ku yi Sallah babu abin da za mu yi muku.
Malam Ibrahim ya ce“Wadansu daga cikin ’yan Boko Haram din suna ta fadin “Allahu Akbar!” Sai suka tunkari wani mai sayar da lemo, suka ce da shi sai ya kai su makarantar boko. Tattara kayansa ke da wuya sai ya faki idonsu ya ruga a guje ya boye cikin wani tamfal da aka rufe dusar dabbobi. A daidai wannan shagon, akwai kantar da ta kwashe yaran ta saka kanta da baya suka kama wani mutum da ya kai su makarantar firamaren Dapchi, wani kuma ya kai su gidajen malaman makarantar. To an ce suna cikin haka ne sai suka ji ihun yaran suka yi wa wadansu kofar rago, suka zuba su cikin motar da suka tafi da su,” inji shi.
Ya ce, “Ina zaune cikin shagon bayan kimanin minti 57 da shigowarsu sai na ga sun dawo, yaran suna ta ihu cikin motar kantar nan. Daga nan na fara rawar jiki domin akwai ’yata a makarantar. Tun da daddare nake neman yarinyar nan har gari ya waye amma ba mu ji duriyarta ba. Daga bisani, ’yar uwarta da ta kubuta ta sanar da da ni cewa, suna tare da ita lokacin da ’yan Boko Haram din suka shigo makarantar. Sai suka rika cewa “Ku zo mu taimake ku kada ’yan Boko Haram su kashe ku, abinka da yara sai suka rika shiga cikin motar. Ita dayar har ta zo za ta shiga sai ta ji wani daga cikin motar yana cewa, idan ba ku yi shiru ba zan yanka ku sai ta juya a guje, wani daga cikinsu ya biyo ta yana cewa idan ba ki tsaya ba zan harbe ki, amma ta ki saurarensa, haka dai Allah Ya tserar da ita.”
Malam Ibrahim Nasiru ya ce, babban abin da ya daure masa kai shi ne, kafin ’yan Boko Haram din su shigo garin Dapchi, mutanen kauyukan da ke kan hanya sun fadi cewa sun ga ayarin ’yan Boko Haram din a hanyarsu ta zuwa garin.
“Tun misalin karfe 3:00 na rana ake kira ana fada mana cewa an ga ’yan Boko Haram din suna zuwa, amma ba su san inda za su je ba. Babu wanda ya kawo wa ransa nan Dapchi za su zo, saboda ba su taba zuwa nan garin ba, ko lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsakani ba su taba kawo farmaki ba. Kusan karfe hudu sai aka shaida mana cewa ayarin Boko Haram din hanyar Dapchi suka biyo. Shugaban karamar Hukuma, Alhaji Zannah Abatcha ya sanar da jami’an tsaro amma ba su dauki wani mataki ba har suka shigo da misalin karfe 6:00 na maraice. Wannan bala’i da muka shiga ba ya misaltuwa, don Allah a taya mu da addu’a,” inji shi.
Sun kama ’yata tana kokarin guduwa – Kabo
Shi kuwa Mohammed Malam Kabo, wanda ’yarsa Fatsuma Muhammed ke cikin daliban da aka sace cewa ya yi, “A lokacin da’yan Boko Haram din suka shiga makarantar suna kokarin sace su da ita da kanwarta da sauran abokan karatunsu, har sun kai bakin get, sai motar ’yan Boko Haram din ta sha gabansu. To a wajen kokarin ta gudu ne sai ta fadi sai suka jefa su a mota, sun tafi mutanen gari na cewa sun ji suna ta ihu amma babu mai taimakonsu. Yaran suna cewa “Don Allah a cece mu La’ilaha ilallah, a cece mu, mun shiga uku.” Tun mutanen gari suna jin ihunsu har muryoyinsu suka bata, na shiga cikin wani yanayi na tashin hakalin da ban taba shiga irinsa ba.”
Ya kara da cewa, “Babban abin tashin hankalin shi ne, bayan kwanakin da muka kwashe cikin juyayi da bakin ciki sai gwamnati ta ce ta gano su. Muka kwana muna murna, amma kashegari aka ce ba a gano su ba. Hakan ya jefa mu cikin wani bakin cikin da bai misaltuwa, wanda sai wanda ’yarsa ke cikin yaran da aka sace ne kadai zai iya ji.”
’Yata ce ta fara shiga motarsu – Bashir Manzo
Alhaji Bashir Manzo, wanda aka sace ’yarsa Fatima ya bayyana wa Aminiya cewa kawayen ’yar sun sanar da shi cewa ita ce ta farko da ta fara shiga motar yayin da ’yan Boko Haram din suka ce su je su taimake su.
“Shigarta ke da wuya sai sauran yaran suka lura cewa silifas ne a kafafun ’yan Boko Haram din, wannan ya sa suka tabbatar cewa ba sojojin gaskiya ba ne. Amma da yake
kaddara na kanta, sai sauran suka gudu suka bar ta. Yanzu haka yaran nan azumi suke yi suna rokon Allah Ya kubutar da ’yan uwansu. Sun ce Fatima ko ruwa ba ta sha ba bayan sun yi azumi ’yan Boko Haram din suka tafi da ita,” inji shi.
Alhaji Bashir Manzo, wanda shi ne Shugaba Gangamin Iyayen da Aka Sace ’Ya’yansu ya ce babu wata tantama ’yan Boko Haram din sun zo ne musamman domin su kwashe yaran. Ya ce, “Saboda ko abincin da ake cewa sun diba a sito din makarantar ba gaskiya ba ne. Sai dai in ’ya’yanmu ne abincin, saboda abincin makarantar yana nan har yau babu abin da ya same shi. Da wannan ina kira ga gwamnati cewa, muna ganin kokarin da take yi amma kuma ta kara. A kuma tsananta bincike saboda babu dalilin da zai sa a ce an janye jami’an tsaro mako daya sannan wannan abin ya faru. Wannan magana abar dubawa ce kamar yadda Gwamna ya ce.”