✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna biyan ’yan bindiga kar su kawo mana hari

Mazauna yankin Shiroro sun koma biyan ’yan bindiga kudade don kar su kawo musu hari.

Mazauna yankunan Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja sun ce suna biyan ’yan bindiga kudade domin kar su kawo musu hari.

Sun bayyana cewa, suna yin hakan ne don su samu damar noma gonakinsu a lokacin damuna mai kamawa saboda ruwan sama ya fara sauka a yankunan.

Al’ummomin sun ce sun fara tattaunawa ’yan bindigar ne kan yadda za su daina kai hari a yankunansu saboda su samu sukunin ci gaba da gudanar da harkokinsu.

Idan ’yan bindigar sun amince, mutanen yankin za su yi kudi-kudi su ba ’yan bindigar, su kuma saya musu ababen hawa da sauran bukatunsu.

Mutanen yankin sun shaida wa BBC Hausa cewa ba su da zabi n da ya wuce tattaunawa da ’yan bindigar domin su samu su kwaci kansu.

Wani shugaban matasan yankin, ya shaidawa Sashen Hausa na BBC cewa yawancin mazauna yankin Garmawa sun jima da sama wa kansu mafita bayan sun yi yarjejeniya da kuma daidaitawa da ’yan bindiga.

A cewarsa, tattaunawa da ’yan bindigar ya zama wajibinsu ne saboda su samu aminci su kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na noma a yankunansu.

“Ya danganta da irin yarjejeniyar da mutanen kowane wuri suka cimma a kai.

“Kowadanne da irin tattaunawar da suka yi da ’yan bindigar, wasu sukan ba su kudi, wasu kuma su ba su babura.

“Muna daukar duk wadannan matakan ne don mu ci gaba da rayuwa cikin aminci,” a cewarsa.

Shi ma wani mazaunin yankin, ya ce sun ba wa ’yan bindigar tsabar kudi Naira miliyan biyu, kuma tun daga lokacin suka fara ganin kyakkyawan sauyi.

“Mun ba su miliyan biyu, kuma mun ganin sauyi da amfanin yin sulhun, magana ta gaskiya ke nan.

“Yanzu mutane na iya gudanar da harkokinsu babu wata tangarda, har su je duk inda suke so,” kamar yadda ya tabbatar.

Jihar Neja na fuskantar matsalolin tsaro daga hare-haren ’yan bindiga da ’yan Boko Haram, wanda hakan ya jefa tsoro da dama a zukatan mutanen Jihar baya ga asarar rayuka da dukiyoyi da suke fama da shi.