✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shirya wa Alhazan Borno gata a Saudiyya – Sheikh Abulfatihi

Shugaban Kwamitin Aikin Hajji na Jihar  Borno, Sheikh Ahmad Abulfatahi Arabi ya ce sun shirya tsaf domin tabbatar da jin dadin mahajjatan jihar. Sheikh Arabi…

Shugaban Kwamitin Aikin Hajji na Jihar  Borno, Sheikh Ahmad Abulfatahi Arabi ya ce sun shirya tsaf domin tabbatar da jin dadin mahajjatan jihar.

Sheikh Arabi ya ce a bana mahajjata 1,723 ne za su sauke farali daga jihar kuma za a kwashe su ne  a zuwa Kasa Mai tsarki a cikin sawu uku, inda ya ce an samu tsaiko a fara jigilar maniyyatan ne wadda ta kamata a fara a ranar Litinin da ta gabata.

“Mun tanadar wa mahajjatanmu masaukai masu inganci a kasar Saudiyya kuma kusa da Harami a Unguwar Shara Mansur, sannan akwai tsarin ciyar da mahajjata a dukkan kwanakin da za su  yi a Kasa Mai tsarki, saboda ba mu fata wani mahajjaci daga Jihar Borno ya samu wata matsala a lokacin aiwatar da aikin hajjinsa. Ta fuskar kiwon lafiya an tanadi jami’ai da magunguna saboda shirin ko ta kwana,’ inji shi.

Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Dokta Mustapha Muhammad ya fada wa wakilinmu cewa, “Mun tantance maniyyatan jihar tare da sanya ido don zakulo wadanda suke dauke da juna biyu, inda har yanzu ba mu samu mai dauke da juna biyu ba. Sannan mun sa ido a kan masu tafiya da abin da hukumomin Saudiyya suka harmta shiga da shi kasar, domin mun hada hannu da Jami’an Shigi da Fici da na Hukumar NAFDAC da kuma jami’an Kwastam don ganin cewa komai yana tafiya yadda muka tsara tun daga tashinsu zuwa Kasa Mai tsarki har zuwa dawowarsu.”

Da yake jawabi a lokacin da ya ziyarci maniyyatan, Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Umar Usman Kadafur ya ba maniyyatan hakuri na tsaikon da aka samu wajen fara jigilarsu, sannan ya yi musu fatan alheri tare da rokon su kasance jakadu nagari.