✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shiga siyasa don magance rikicin kabilanci a Legas- Ahamad Kabir

Alhaji Ahmad Kabir shi ne babban magatakarda na ma’aikatar kula da ruwa na Jihar Legas kana shugaban kungiyar ‘yan Arewa mazauna Jihar Legas sannan jigo…

Alhaji Ahmad Kabir shi ne babban magatakarda na ma’aikatar kula da ruwa na Jihar Legas kana shugaban kungiyar ‘yan Arewa mazauna Jihar Legas sannan jigo ne a jam’iyar APC a Legas, a zantawar sa da Aminiya ya zayyana nasarorin da  ma’aikatarsa ta yi ta fuskar inganta ruwan sha a Legas da dalilan da ya sanya suka shiga siyasar Legas dama  rawar da ‘yan Arewa mazauna Legas ke takawa a siyasance

Aminiya: Zamu so ka gabatar da kanka

Ahmad Kabir: Sunana Acitek Ahmad Kabir a nan Legas aka haife ni anan na taso ko da yake ni bafulatanin Daura ne, a Legas na yi karatun firamare da sakandare daga nan na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1986 na yi karatun share faggen shiga jami’a daga nan na yi karatun digiri na na farko a fannin zane da tsara fasalin gine-gine daga shekarar 1987 zuwa 1990 sannan na tsaya na ci gaba da karatun digiri na na biyu a dai fannin zane da tsara fasalin gine-gine wanda ake kira acitekta a turance na kammala digiri na na biyu a shekarar 1992 bayan na kammala yiwa kasa hidima a shekarar 1993 sai na fara aiki da wani kamfani mai zaman kansa na gine-gine a birnin Legas har na kai ga matsayin manajan kamfanin kafin daga bisa ni na koma harkar siyasa  na fito  takarar shugaban karamar hukumar Agege daga baya aka sasanta mu na janye na tsaya matsayin mataimakin shugaban karamar hukumar daga shekarar 1996 zuwa 1997 lokacin ne aka rushe tsarin siyaysa kafin daga bisani a kafa sabuwa a shekarar 1999 inda Dokta Ahmad Bola Tununbu ya zama gwamnan Jihar Legas ya nadani shugaban hukumar da ke kula da tsare-tsare na birnin Legas tare da kare muhallinta a shekarar 2001, lokacin da Babatunde Fashola ya zama gwannan Legas sai ya karamin girma a ma’aikatar ya mayar dani babban manajan wajan sannan kuma da gwamnan mu na yanzu yazo gwamna Akinwumi Amode sai ya nada ni babban magatakarda na ma’akatar kula da  tsare-tsaren harkar ruwa a Jihar Legas wato ‘Legas state water regulatari komishin’ wanda shine mukamin da nike a yanzu.

Aminiya: Ko me yaja ra’ayinka  ka shiga siyasar Legas? 

Ahmad Kabir: Alal hakika mun yi siyasa irin ta makaranta sai kuma aka yi wani lokaci a nan cikin garin Agege an sami matsaloli na zamantakewar jama’a abin da ya shafi rigingimu na kabilanci tsakanin yarbawa da hausawan,  wannan ya kashe wannan, wanccan ya kashe wannan, nan fa  muka yi amfani da shawarar da marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya taba bai wa iyayen mu lokacin da yazo nan Legas inda suka nuna masa goyon bayansu sai ya basu shawara yace su yi siyasa irin ta wadanda suke zaune da su, domin in ka nuna kana kyamar mutum sai shima ya ƙi ka amma duk mutumin da kace kana yi dashi to zai so ka,  sai muka ga shiga cikin harkokin siyasa tare da hulda da shuwagabannin yarbawa kai tsaye  kai domin hakan ne zai magance mana matsalar mu, haka kuwa a ka yi har muka kafa kungiyar sassanta tsakani tare da yin sulhu da yafe wa juna a haka muka yi sabo da juna inda muke zama da shuwagabannin kungiyoyin su da na ‘yan siyasa a haka har ta kai ga na tsaya takarar shugban karamar hukuma aka zauna aka daidai ta suka nemi na janye masu su bani mataimaki na hakura da hakan kuma Allah cikin Ikon sa muka tsaya zabe muka kuma yi nasara.

Aminiya: Kana ganin kwalliya ta biya sabulu biyo bayan siyasar da kantsunduma? 

Kabir Ahmad:  Alhamdulillahi tun daga wanccan lokaci kwalliya ta biya kudin sabulu domin mun sami zaman lafiya da fahimtar juna, saboda a da baka isa ka sanya  doguwar riga da hula ka yi yawo a Legas yadda kake so ba, amma ga shi a yanzu damu ake damawa, mun samarwa da yawa daga cikin matasan mu guraben ayyukan yi a matakin kananan hukumomi da jiha, sannan akwai yaran mu da dama da suka tsaya takarar kujerun kansiloli suka ci zabe, duk sanda tallafi yazo wanda za a baiwa mata ko nakasassu muna yin duk abin da ya kamata domin na  mu su amfana don ko kwanakin baya ma akwai tallafin jari da gwamnatin Legas ta bai wa nakasassu kimanin mutun 500 ‘yan Arewa suka amfana a rukuni  na farko ana kuma shirya bai wa kaso na biyu, don haka akwai alfanu da dama duk da a lokacin da muka shiga aka fara gwagwar mayar siyasar da mu  mutane da yawa na yi mana kallon ‘yan iska wasu kuma suna ganin kamar lokacin mu kawai muke batawa inda a wancan lokacin mutanen mu na ganin marasa mutumci ne ke shiga siyasa don ba zan manta ba har aure na nema aka hana ni saboda muna yin harkar siyasa sai dai mu gode wa Allah domin Allah ya sanya wa abin albarka jama’a da dama na cin gajiyar abin, kuma siyasar mu ce silar hadewar shugaba Buhari da Asiwaju Ahmad Bola Tuninbu domin ba zan manta ba a lokcin nan sau biyar muna zama da shugaba Buhari a kan maganar, da muka zauna Mamman Daura haka batun hadewar har ya ke fadamin ta yaya zan gansar dasu in hakan zata yi aiki a haka na fayyace masa tsarin mu don muba wanccan lokacin manufarmu ma idan an hade Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa Tinubu ya yi masa mataimaki, haka muka yi ta yi muka je wajan Buhari sannan muka je wajan Tinubu da farko dukkan sunsun ki ko wanne ya nuna rashin gamsuwar sa da dayan sai muka koma muka zuga sanata Abu Ibrahim sannan muka hadu mu 45 muka je Bargu wajan marigayi mai martaba sarkin Bargu na wanccan lokacin Haruna Dantoro  Allah Ya jikan shi ya ce gaskiyane abin da kuka fada din nan, ni zan nemin Buhari zan kuma nemi Bola Tinubu aka zo ana wani biki ya gayyace mu ya kira Buharin da Tinubu ya hada su don hakanmu ba abin da zamu cewa siyasa sai alhamdulillahi.

Aminiya: Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta Jihar Legas da kake jagoranta ko ya take gudanar da aikin ta?

Ahamad Kabir: Hukuma ce da take kula da albarkatun ruwa na Jihar Legas, ita ke bada dama ko lasisi idan mutum yana so ya yi hada-hadar kasuwanci na ruwa abin da ya shafi ruwan sha da na amfanin masana’antu mu ke bincike mu bada damar hakar rijiyar burtsatse a inda ya dace domin a samar da tsaftataccan ruwa, mu ke kulawa ingancin ruwa da gurbatancen ruwa da dagwalon masana’antu inda muke tabbatar da ba a zubar da ruwa mai dauke da guba daga masana’antu zuwa muhallinmu domin bada kariyar muhalli, wannan hukuma na samar da hanyoyin sarafa irin wannan dagwalo ta yadda bazai kawo cikas ga muhalli ba.

Aminiya: Ko akwai nasarorin da ka samu kawo yanzu da jan ragamar wannan ma’aikata ta ruwa?

Eh Alhamdulillahi zuwa na na rubbanya kudaden shiga da wannan masana’antar ke samu da kaso sama da 700, mun yi nasarar hakan ne ta wayarwa al’umma kai musanmman masu sha’awar zuba jari a harkar ruwa domin sana’a ce mai dinbin riba, muna wayar wa jama’a kai su yi aiki tare damu domin inganta sana’ar su, a irin wannan nasara ne ya sanya a yanzu muna fita da ruwan sha daga nan Legas zuwa kasashen ketare saboda irin ingantancen ruwa da muke samarwa wanda kasashen duniya suka yi amanna da shi, kuma burin mu anan gaba shi ne bai wa masana’antu masu zaman kansu damar samar wa jama’a ingantanccen ruwan famfo wanda a yanzu mun yi nisa da aikin a rukunin gidajen cikin birnin Legas na Biktoriya Ailan.