✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kafa kungiyar Talaka Zalla ne domin taimakon marasa karfi – Alhaji Helle

Shugaban kungiyar Talaka Zalla na Jihar Katsina ya ce sun kafa kungiyarsu ne domin taimakawa marasa karfi. Alhaji Halle Ma’azu Tudun ‘Yan shanu ya bayyana…

Shugaban kungiyar Talaka Zalla na Jihar Katsina ya ce sun kafa kungiyarsu ne domin taimakawa marasa karfi.

Alhaji Halle Ma’azu Tudun ‘Yan shanu ya bayyana tarihin kafuwar wannan kungiya, inda ya ce “Ina bai wa gajiyayyu taimako ne a duk ranar Juma’a. Mafi yawan abin da nake ba su sun hada da abinci da tufafi. Kuma ina bai wa duk wanda yake mabukaci ne ba tare da la’akari da bambanci ba. 

“To wannan taimako da nake yi wa bayin Allah, sai suka fara kira na da shugaban talakawa. Da farko na nuna bana son wannan kalma, amma kuma dole na hakura domin su wadannan talakawan ne da kansu suke kira da wannan suna”.

Shugaban daga nan sai ya ce ganin yadda su takalawan suke fadin kalmar shugabancin sai ya yi tunanin cewa yana da kyau a kafa kungiya domin su. Haka kuma aka yi “Mun kafa kungiya kuma duk abin da ake yi na kafa kungiya babu abin da muka rage. Hatta ofis duk muna da shi, kuma mun sanya mata sunan “kungiyar Talaka Zalla” saboda an kafa ta ne domin taimakawa talakan. 

Alhaji Halle ya ci gaba da cewa kungiyar ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka kafa ta domin su. Taimakon da ya shafi samar wa irin wadannan marassa karfi abin yi. Taimakawa marayu hatta ta fuskar ilminsu da sauran wasu abubuwan rayuwa na yau da kullum. 

Shugaban kuma ya ce har gobe basu bari harkokin siyasa su shigo cikin harkokin kungiyarsu. “Akwai ‘yan siyasar da suka yi kokarin shigowa acikin kungiyar ta hanyar kawo gudunmuwarsu, amma saboda sanin halinsu ya sanya muka ki bayar da kofa. Amma ba wai muna nufin ba zamu karbi tallafin jama’a ba, a’a, sai wadanda muka san zai yi domin Allah kuma in ya kawo a rarraba taimakon nan a gabansa domin Allah.

Shugaban ya ce duk dokoki da ka’idodin da ake bi na kafa kungiya sun bi, kuma suna da duk wata takardar da ake nema. Kuma suna yin ayyukan kungiyarsu ba tare da damuwar jama’a da yin bara ba, saidai wanda ya ga dama domin Allah zai iya kawo tashi gudunmuwar kofarsu a bude take.

Kafin tattaunawa da shi shugaban wannan kungiya, sai da Aminiya ta ji ta bakin wata baiwar Allah wadda ta nemi a boye sunanta, inda ta shai da cewa wannan kungiya ta Talakka Zalla ita ce ta zamo uba ga marainiyar diyar ta “Na yi mamakin yadda har wannan kungiya ta san akwai mu, da kuma irin halin da muke ciki. Kawai sai dai ake ce mani in zo wasu mutane na son gani na. Bayan na zo wajensu, sun yi mani wasu ‘yan tambayoyi dangane da batun auren diyata wadda kuma take marainiyace, wallahi sai dai kawai na ga an kawo kayan daki da duk wasu abubuwan da ni ban ma iya tuna su. Hatta kayan kallo sai da aka sanya a dakin wannan yarinya.

“Kuma sai daga baya ma nasan shi wannan shugaba, sannan kuma aka ce kungiya ce ta yi mani wannan taimako saboda Allah. Kuma har zuwarka nan a yanzu yau shekara biyu ke nan da ‘yan watanni har ma aure ya yi albarka, amma babu wani wanda ya zo daga baya ya ce ga wata bukata da wannan kungiya take nema daga gare mu”.

 Akwai mutane da dama da Aminiya ta zanta da su a kan ayyukan wannan kungiyam kowa na san barka. Wasu daga cikin mutanan da muka zanta da su, shawara suka ba gwamnati da ma masu hannu da shuni da cewa a duk lokacin da za su bayar da kayan tallafi, su rika ba irin wannan kungiya ta raba domin zai kai ga hannun mabukatan.