✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Mun gano wadannin macizai a dajin Ecuador —Masana

Tsawon nau'in wadannin macizan sanitimita 20 (kimanin inci bakwai)

Masana kimiyya sun gano wadannin macizai masu tsawon sanitimita 20 (kimanin inci bakwai) a kasar Ecuadora.

Ma’aikatar muhalli ta Ecuador ta ce ce an gano wadannin macizan guda biyu — masu kama da nau’in Boa Constricptor — ne a gandun dabbobi na Colonso Chalupas da ke Kudancin kasar.

“Wannan nau’in ya zo da sabon salo a halittarsa, domin sabanin sauran macizai yana da kashi a kasan cikinsa.

“Wannan shaida ce cewa wasu macizan asalinsu daga kadangarun da suka rasa gabobinsu ne miliyoyin shekaru da suka gabata,” a cewar binciken.

Wani mai bincike a cibiyar kula da halittu ta kasar (INABIO) Mario Yanez ya shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na (AFP) cewa macizan burbushin tarihi ne saboda tsufansu, ta yadda gano su din ya zamo wata babbar alfarma.

Masana kasar sun sanya nau’in wadan macijin sunan wata tsohowar ’yar gwagwarmayar kasar Dolores Cacuanga.

An dai buga sakamakon binciken a Jaridar kasar ta Taxonomy.