Shugabannin jam’iyyar APC daga jihohi 7 na yankin Arewa maso Yamma sun ce suna goyon bayan a ba tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, shugabancin jam’iyyarsu na kasa.
Matakin ya biyo bayan kammala wani taro da shugabannin suka yi ranar Laraba a Kaduna.
- ’Yan majalisar Ghana sun amince a cire hukuncin kisa a kasar
- Fadar Shugaban Nijar ta ce yunkurin juyin mulki ga Bazoum bai yi nasara ba
A cewar takardar bayan taro da shugabannin suka fitar, sun ce sun yanke shawarar goyon bayan Gandujen ne saboda irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen nasarar jam’iyyar a baya.
Takardar dai na dauke ne da sa hannun dukkan shugabanni bakwai da suka hada da Hon. Isa Sadiq Acida (Sakkwato); Emmanuel K. Jekada (Kaduna) ; Hon. Abubakar Muhammad Kana (Kebbi), Abdullahi Abbas (Kano); Hon. Aminu Sani Gumel, (Jigawa); Hon. Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da kuma Hon. Muhammad Sani Ali, (Katsina).
A cewarsu, tsohon Gwamnan na Kano ba ƙashin yarwa ba ne la’akari da irin rawar da ya taka wajen samun nasarar Shugaban Kasa mai ci, Bola Tinubu.
“A matsayinmu na shugabannin jam’iyya mai mulki a jihohinmu, mun yi dukkan nazarin da ya dace, inda muka amince cewa indai cancanta za a duba da sanin aiki da kwarewa da sani ya kamata da kuma jajircewa, to tabbas Ganduje ne ya fi dacewa ya jagoranci jam’iyyarmu, ba wai kawai a matakin shiyya ba, har ma da kasa baki daya,” in ji Shugabannin.