✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mummunan hadarin mota ya ci mutum 28 a Bauchi

Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC reshen jihar Bauchi ta ce, mutum 28 suka mutu bayan sun kone kurmus a wani mummunan hadarin mota da…

Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC reshen jihar Bauchi ta ce, mutum 28 suka mutu bayan sun kone kurmus a wani mummunan hadarin mota da ya faru a kauyen Gubi Gari da ke babbar hanyar Bauchi zuwa Kano a yau Alhamis.

Kwamandan Hukumar FRSC shiyyar Bauchi, Abdulrazak Najume, ne ya sanar da hakan ga manema labarai, inda ya ce hadarin ya auku ne tsakanin wasu motoci biyu daya  mota bas kirar Peugeot J5 da kuma wata motar bas kirar Toyota Hiace mai kujeru 18 wanda take da lamba kamar haka: ZRM-91XA.

Daya daga cikin motar ta kone kurmus lokacin hadarin.

Abdulrazak Najume,  ya kara da cewa a cikin fasinjoji 29 da hadarin ya rutsa da su daya ne kawai ya rayu.