✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman alkaluma daga rayuwar Sarki Charles III

A ranar Juma’a Charles ya yi cikakken wuninsa na farko a matsayin Sarkin Ingila.

Rasuwar Sarauniyar Ingila ke da wuya, sai mulkin ya koma kan danta magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin nadin sarauta ba.

Amma akwai matakai na al’ada da dama da za a taka kafin a tabbatar da shi.

Charles, wanda ranar Juma’a ya yi cikakken wuninsa na farko a matsayin Sarki bayan mutuwar mahaifiyarsa marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth II, ya shafe tsawon rayuwarsa yana jiran gado.

Ga wasu muhimman alkaluma daga rayuwar Sabon Sarkin Ingila Charles III:

  • 2

Sau biyu yana kamuwa da cutar COVID-19. A watan Mayu na 2020 an gwada shi kuma aka tabbatar da cewa ya kamu da cutar, hakan ya sa ya killace kansa na tsawon mako daya.

Sai a watan Febrairu na bana da ya sake kamuwa da cutar.

  • 3

Shekarunsa a duniya lokacin da ya zama na farko a jerin masu gadon sarautar Ingila bayan kakansa George VI ya rasu a shekarar 1952. A lokacin ne mahaifyarsa Elizabeth II ta zama Sarauniyar Ingila.

  • 4

Shekarunsa lokacin da ya fara tsaga gashin kansa; lamarin da ya zame masa wata al’ada ta kwalliya kuma ya zame masa jiki.

  • 11

Adadin Shekarun da Charles  ya yi  tare da tsohuwar matarsa Diana Spencer, wacce suka rayu a matsayin miji da mata daga shekarar 1981 zuwa 1992; suka kuma rabu a 1996.

Charles da Diana ranar aurensu
Yarima Charles da tsohuwar matarsa Gimbiya Diana ranar aurensu 29 ga watan Yulin 1981

Matar tasa ta dora alhakin mutuwar aurensu a kansa, saboda ma’amalarsa da Camilla Parker Bowles.

  • 27

Adadin wasikun da ake wa lakabi da “black spider memos” wadanda ya tura wa Gwamnatin Tony Blair a shekarar 2004-2005.

A wasikun, Charles ya bukaci gwamnatin da ta dauki matakai a kan rashin samar da isassun kayan aiki tare da tura su ga sojojin ruwan da ke  tekun Patagonia.

  • 52

Adadin shekarun da motarsa kirar Aston Martin DB6, wadda daga bisani a shekarar 2008 ya mayar mai amfani da makamashin bioethanol wanda aka sarrafa daga bammi da cukwi, ta yi a hannunsa.

Yarima Charles tare da motarsa kirar Aston Martin DB6 (Hoto: yahoo.com

A motar babban dansa Yerima William ya fita daga Fadar Buckingham tare da amaryarsa bayan an daura aurensu a shekarar 2011.

  •  350

Shekarun da wani kamfanin tufafi a Worcester da ke tsakiyar Ingila ya kwashe kafin a biya shi kudin da yake bin Sarki Charles II Fam 453.15 (kwatankwacin dalar Amurka 527 a yanzu). Kamfanin ya dinka kakin soji tun a karni na 17.

Yariman, wanda ya zama Charles na III ranar Alhamis, shi ya biya bashin ba tare da kudin ruwa ba a shekarar 2008.

  •  3,344

Adadin tan na gurbatacciyar iskar carbon dioxide da Charles da Camilla suka fitar a shekara guda da ta kare ranar 31 ga watan Mayu, 2019.

Sarkin, wanda mutum ne mai fafutukar kare muhalli, ya sha suka saboda yawan amfanin da yake yi da Jirage na kashin kai yayin tafiye-tafiyensa.

  • 1,000,000

Adadin mutanen da suka ci gajiyar gidauniyar Prince’s Trust, wadda Charles ya kafa a 1976 da kudin sallamarsa daga Rundunar Sojin Ruwa [Birtaniya].

Ya kafa gidauniyar ne domin tallafa wa matasa daga unguwannin marasa galihu.

Har ila yau wannan ne adadin gudunmawar da Charles ya karba daga dangin mutumin da ake zargi da kitsa harin 9/11, Osama Bin Laden, a 2013 don gudanar da gidauniyar.

  • Miliyan 1.6

Adadin mabiyan Charles da Camila a shafin Instagram. Idan aka kwatanta, Yarima William da Kate suna da mabiya miliyan 13.9.

 An samo wadannan alkaluma ne daga Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP).