✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa 10 game da sabon shugaban ABU

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da zaben Farfesa Kabir Bala a matsayin sabon shugaban Jami’ar. Hukumar ta sanar da…

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da zaben Farfesa Kabir Bala a matsayin sabon shugaban Jami’ar. Hukumar ta sanar da cewa, sabon shugaban zai fara aiki ne a matsayin sabon shugaban jami’ar daga ranar 1 ga watan Mayu 2020.

A binciken da Aminiya ta yi ta gano wasu muhimman abubuwa 10 game da sabon shugaban jami’ar ABU Zariya, wadanda suka hada da:

  1. Sabon shugaban ya fi sha’awar a kira shi da suna ‘Malam’ a maimakon Farfesa.
  2. Farfesa Kabir Bala, ya wallafa mujallu da kasidu sama da 80 a Najeriya da kasashen waje.
  3. Yana daya daga cikin masu zabar, masu zama Farfesa a sama da jami’o’i bakwai a Najeriya.
  4. An haife shi ranar 7 ga Janairun 1964 a Unguwar Kanawa, jihar Kaduna ya kasance kwararre a fannin gine-gine, sannan Farfesa a harkar gine-gine.
  5. Hakazalika a watan Oktoba 2013, an nada shi mamba a Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC).
  6. Ya rike mukamin shugaban tsangayar koyar da gine-gine sau biyu daga 2001 zuwa 2006 sannan kuma daga 2010 zuwa 2014. Shi ne na farko da ya fara jagorantar kafa ilimin fasahar sadarwa ta jami’ar ABU (ICT).
  7. Ya yi makarantar firamare a Unguwan Sarki, Kaduna sannan ya wuce zuwa Kwalejin Barewa Zariya, inda ya kammala a shekarar 1981. Ya fara karatun share fagen shiga jami’a wato (IJMB) na cibiyar jami’ar ABU, sannan ya wuce zuwa jami’ar Ahmadu Bello Zariya ya samu shaidar digirinsa na farko a fannin gine-gine (Building) a shekarar 1985.
  8. Ya karantar da dalibai da dama masu karatun digiri na farko da na biyu, tare da duba dalibai masu nazari akan shaidar digiri ta biyu (Master’s) dalibai 30 da kuma sama da dalibai 10 masu nazari akan shaidar digiri ta uku (Phd).
  9. Shugaba Buhari ya nada shi a matsayin shugaban hukumar masu yin rijistar magina ta kasa (CORBON) saboda ci gaban da ya kawo a harkar gine-gine.
  10. Ya kasance mai taimakawa a matsayin malamin jami’a a shekarar 1990, ya zama cikakken malamin jami’a II a shekarar 1993, malamin jami’a mai daraja ta daya a shekarar 1998, babban malamin jami’a a shekarar 2001, mai nazari a 2004 sannan ya zama Farfesa a shekarar 2007.