✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu yawaita addu’a ga shugabanni kan matsalolin ƙasa -Sarakunan Samarin Oyo

Majalisar Sarakunan Samarin Hausawa a Jihar Oyo ta ce yawaita roƙon Allah Ya yi wa shugabannin ƙasa jagoranci ne hanya ta farko wajen samun sauƙin…

Majalisar Sarakunan Samarin Hausawa a Jihar Oyo ta ce yawaita roƙon Allah Ya yi wa shugabannin ƙasa jagoranci ne hanya ta farko wajen samun sauƙin rayuwa a Nijeriya.

Kuma hakan zai taimaka wajen lalubo hanyar magance matsalolin tsaro da suka dabaibaye ƙasar.

Majalisar ta ce bai kamata kalaman ɓatanci da tsinuwa ga shugabanni su riƙa fitowa daga bakin mutane ba, domin yin hakan na taimakawa ne wajen ƙaruwar matsaloli a maimakon samun mafita.

Shugaban Majalisar Sarakunan Samarin kuma Sarkin Samarin Ogbomoso, Alhaji Ahmed Bello, ne ya faɗi haka a ranar Lahadi bayan taron da majalisar ta yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Ya ce “Sarakunan Samarin Hausawa daga sassan jihar ne suka halarci wannan taron gaggawa domin tattaunawa a kan matsayinmu dangane da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka fara yi.”

Ya ce “Taron ya amince cewa tubalin ginin ƙasa na biyu shi ne dukan shugabanni Musulmi da Kirista da mabiya wasu addinai da suke riƙe da muƙamai tun daga kan kansila zuwa Shugaban Ƙasa su sa tsoron Allah a zukatansu kuma su riƙe amanar jama’a da Allah Ya damƙa a hannunsu.

“Irin  waɗannan shugabanni tun suna raye a duniya Ubangiji zai fara yi masu hukunci ta hanyar da ba su sani ba, idan suka ci amanar ƙasar haihuwarsu,” in ji shi.

“Lokaci ya yi da shugabannin ƙasa za su jingine amfani da siyasa wajen rabon tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa ga jama’ar ƙasa musamman matasa.”

Muhimmin abu na uku da taron majalisar ke ganin zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin ƙasa shi ne matasa musamman a Arewa su ƙara yin haƙuri da matsin rayuwa su miƙa al’amuransu baki ɗaya ga Ubangiji.

Majalisar ta nemi matasan su tashi tsaye wajen neman abin dogaro da kai kuma su daina raina ƙananan sana’o’i da ayyukan yi, su roƙi Allah Ya sa albarka a kan dukkan abubuwan da suka sa a gaba.

Shugaban  Majalisar Sarakunan Samarin ya ce “Duk da yake matasan Hausawa da ke zaune a Jihar Oyo sun yi aiki da umarnin shugabanni suka yi zamansu a gidaje da wuraren ayyuka a ranar da aka fara zanga­zangar amma mun goyi bayan zanga-zangar lumana da ake yi a wannan jiha. Mun ɗauki wannan mataki ne domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Oyo da ƙasa baki ɗaya.”

Ya ce matsalolin matasan Arewa sun bambanta da na Kudu domin a Kudu za ka ga matashi namiji ko mace na koyon ƙananan sana’o’i da ayyuka daban-daban saɓanin Arewa da ba a samun irin haka.

Saboda haka majalisar ta yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19 da Gwamnatin Tarayya su yi da gaske wajen lalubo hanyar magance matsalolin da matasa suke ciki a yanzu.