✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Dan wala wala

Lallai asiri gaskiya ne.

Wani dan walawala ne ya je wata kasuwa a Nijar shi da yaransa.

Ya tara Buzaye yana walwala masu karta, yana cewa duk wanda ya dauko fara marar zane, Jika 5 a Jika 50.

Sai ’yan korensa suka rika zuwa da Jika 5 suna cin 50.

Ko da Buzaye suka gani sai suka fara sa kudi yana cinyewa, sai da ya amshe masu kudinsu duka.

Ya fara nade kayansa sai Buzaye suka fara zaro takobi suka zagaye shi, suna cewa ya mayar masu da kudinsu ko su kashe shi.

Ai ko da yaransa suka ga haka sai daya ya zo ya ce shi ma sai ya ba shi kudinsa Jika 200 ko a kwashi ’yan kallo.

Su kuma Buzaye ba su san tare suke ba.

Ko da dan wala-walan ya ga yaron nasa sai ya ce masa: “Kai Malam, tube rigarka.”

Sai ya tube. Ya sake cewa: “Tube wandonka.”

Ya tube, ya yi zindir. Sai ya ce masa: “Shiga dawa.”

Sai ya ruga da gudu. Su kuma Buzaye ba su san yaudarar su aka yi ba.

Sai dan walawala ya kalli Buzaye, ya ce masu: “Duk wanda ya kara maganar kudi, haka zan mai da shi.”

Take suka tsorata, kowa ya mayar da takobinsa cikin kube, suna cewa: “Lallai asiri gaskiya ne.”