✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Motar Sale Wadansu samari biyu ne suka tafi ci-rani birni kuma dama an gaya musu cewa akwai wani mai kudi daga kauyensu da yake zaune…

Motar Sale

Wadansu samari biyu ne suka tafi ci-rani birni kuma dama an gaya musu cewa akwai wani mai kudi daga kauyensu da yake zaune a birnin, sunansa Sale. Suna cikin tafiya a birnin sai suka ga wata mota an rubuta cewa: “This car is for Sale” (Wannan motar ta sayarwa ce). Sai dayan ya kalli abokinsa ya ce masa: “Kai, duba can ka gani, waccan motar ta Sale ce, da ma an ce yana da motoci da yawa a garin nan.”

Daga Maryam Abdulrashid Jaji, 07032366792

 

Ci ka sha amma …

A wani otel ne a Katsina, aka rubuta a jikin allon sanarwa cewa: “Ka ci, ka sha iya yinka, amma jikanka ne zai biya kudin. Wani Bahadeje da ya ga haka sai ya shiga otel din, domin dai ya san cewa ba ya da aure balle jika; wato zai ci banza ya tafi. Bayan ya ci abinci ya gama sai ya ga daya daga cikin ma’aikatan otel din ya kawo masa takardar adadin kudin da zai biya. Bahadeje ya ce: “Yaya haka? Ku fa kuka ce jikana ne zai biya kudin.” Ma’aikacin ya ce masa: “Ai dama ba kudin da ka ci ne za ka biya ba, na kakanka ne da ya ci za ka biya, ga shi can a zaune!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

 

Tsohon soja

Wani Banufe ne dan limami ya tafi aikin soja, da ya gama aikin ya dawo gida, mutane suka rika ce masa: “Sai ka yi liman.” Shi kuwa yana cewa amin. A kwana a tashi, ran nan sai Allah Ya yi wa liman rasuwa sai mutanen gari suka ce: “Ai ga tsohon soja dan liman, a kira shi a yi masa tambaya a kan matsalar Sallah; idan ya amsa sai a nada shi, ya gaji babansa.” Da ya zo sai aka yi masa tambaya a kan kabli da ba’adi, aka ce masa idan mutum yana cikin Sallah sai kabli da ba’adi suka kama shi yaya zai yi? Sai Banufe tsohon soja ya ce: “Ai ni ba zan aikata laifin da zai sa su kama ni ba kuma ko sun kama ni sai in tuna aikin soja, in gama da su.”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi,

Babarbare da Bafulatani

Wani Babarbare ne da Bafulatani suka fita yawo wajen gari, sai wadansu  azzalumai suka kama su, suka kai su wajen shugabansu. Shi kuma sai ya nuna musu wani lambu ya ce su shiga su tsinki duk dan itacen da suke so. Bayan wani lokaci sai ga Bafulatani ya fito da manya-manyan mangwarori biyu a hannunsa. Nan take shugaban ya ce da yaransa su danne shi su sanya masa mangwarorin a duburarsa. Take suka cika umarni, Bafulatani ya sha bakar wuya. Ya daga kai ke nan sai ya hango Babarbare, sai ya kece da dariya. Da aka duba don a ga abin da yake yi wa dariya, sai aka ga ashe Babarbare ne ya tsinko manya-manyan kabewa biyu a hannunsa yana tahowa.

Daga Jibril Ali Haidar Badawa, Kano 08095655514