✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu sha dariya

Santin Sakkwatawa Wasu Sakkwatawa ne aka dama masu hura suna sha, kowa ya kama ludayi daya-daya, da aka kai zagaye na karshe; da ya kandamo…

Santin Sakkwatawa

Wasu Sakkwatawa ne aka dama masu hura suna sha, kowa ya kama ludayi daya-daya, da aka kai zagaye na karshe; da ya kandamo ludayi sai ya ce: “Hhmmn, umaru shin wai gero yana esfiya ne?” Sai daya daga ciki ya ce: “Bello ni ma dai abin da nake so na tambaya ke nan!”
Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 07066581437

Mahaukaci da Fasinja

Wata rana wani mutum zai je wurin aiki ya makara, yana jiran mashin sai ga wani dan achaba a guje. Nan take mutumin nan ya tsaida shi, ashe mahaukaci ne bai sani ba. Mahaukaci ya dauki mutumin yana ta sharara gudu, can sai wata danja mai tsaida abin hawa ta tsaida su. Mutumin sai ya ji mahaukaci na haki yana cewa: “Da kyar na nemo birki, jiya kamar yanzu ina Kyoto ban san inda birki yake ba.”
Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa, 08034208356

Dan a rufta

Wasu ’yan sholisho ne suna cikin shan abinsu, sai daya ya dubi dayan ya ce: “Anya za mu shiga aljanna kuwa?” Sai dayan ya ce: “Yo ai abin taget ne. Ga jama’a da yawa, kawai da ka faki idon walakiri sai ka rufta ciki, kawai ka yi fuska!”
Daga Rayyan Jada

Wasa ko zolaya?

Wani Bakatsine mai suna Buba ya zubar da kudi sai ya zo yana ’yan dube-dube, amma bai dai yi cigiya ba. A wurin akwai wani Bahadeje mai suna Ilu, sai ya kada baki ya ce wa Buba: “Kudi ne ka zubar cikin bakar leda nan wurin? ‘Yan Naira dubu guda 3 ko? An daure su da tsumma? Sabbi ne ko?” Buba ya ce: “Eh, su ne kuwa!” Sai Ilu ya ce: “Ban gan su ba!”
Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933