✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu rika kula da mutuncin kanmu

A wannan mako mun dauko wani rubutu ne daga Kundin Solana Olumhense da jaridarmu ta Ingilishi Sunday Trust ta farkon wannan mako ta buga, inda…

Alhaji Shamsudeen Usman tsohon Ministan Tsare-TsareA wannan mako mun dauko wani rubutu ne daga Kundin Solana Olumhense da jaridarmu ta Ingilishi Sunday Trust ta farkon wannan mako ta buga, inda ya yi sharhi kan korar ministoci tara da Shugaba Jonathan ya yi a makon jiya. Marubucin ya tabo batun jami’an gwamnati su koyi dabi’ar tsira da mutuncinsu tun kafin a zubar musu da shi a kasuwa:
A makon jiya ne aka kori ministocin Najeriya tara wadanda rikicin shugabancin da ke addabar jam’iyya mai mulki PDP ya jawo musu haka. Abin takaici an sallami ministocin ne ba domin a inganta majalisar zartarwar ba. Da saboda haka ne ministoci da dama za a sallama.
Abin da girgizawa ganin yadda aka tozarta Ministan Tsare-Tsaren kasa Shamsudeen Usman. A wani rubutu da na yi a watan Maris din 2012, na nemi kada ya jira sai an sallame shi, saboda gwamnatinsa ta yi karya game da shirinta na sake fasalin kasa da Ministan ya shaida wa ’yan Najeriya su sa rai a kai a watan Oktoban 2011.
Malam Usman ya ce shirin zai magance matsalolin rashin da’a da ke addabar kasar nan. Ya shaida wa manema labarai cewa: “A cikin dukkan al’ummu, idan ba ka da tsarin da ke kamawa ya hukunta wadanda suke saar dukiyar jama’a, to za su ci gaba da yin satar.  Wadannan suna daga cikin abubuwan da shirin sake fasalin kasa zai magance… Wajibi ne mu karfafa bin doka da inganta bangaren shari’a da aikin dan sanda. Idan ka san akwai dama kashi 99 cikin 100 na a kama ka idan ka yi sata, kuma akwai kashi 100 na tabbacin za ka tafi kurkuku, ba za ka yi satar ba.”
Sai dai wannan ba gaskiya ba ne. Wannan shiri da ake kira na sake fasalin kasa ya saba kwata-kwata da wannan yunkuri na magance wadannan matsaloli. Ya bayyana a fili cewa wani mamunga ne aka shirya domin yaudarar talakawa da masu rauni.
Abin da yake fili shi ne zamanin “Shirin Sake Fasalin,” sabanin yyadda tsohon Ministan ya nuna, baun bin doka da oda ya zama abin ba’a. Saboda idan muka leka wani gefen za mu ga idan ka yi babbar sata, akwai tabbaci 100 bisa 100 za a ba ka lambar yabo ta kasa, ba daurin da za a I maka kamar yadda lamarin Dipreye Alamieyeseigha ya nuna. Shirin Sake Fasalin kasar ya tabbata gangariyar 419: ga dadin fada, amma idan ka kale shi labarin kanzon kurege ne.
Wannan ne ya san a I faa Usman, a matsayinsa na dalibin mashahuriyar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da Makarantar Tattalin Arziki da Kimiyyar Siyasa ta Landan, zai gane ya saba alkawarinsa ya sauka daga mukaminsa.
Amma bai gane ba, balle ya sauka. Haka wannan tabargaza ke ci gaba, wasu manyan jami’an gwamnati suna ta sakin baki suna lullube gaskiyar lamari kan wannan shiri na yaudara. Ta hanyar ci gaba da zama a gwamnati, Usman ya taimaka a cimma nasarar wannan munfunci, koda kuwa bai taimaka wajen shirya shi ba. Sai ga shi a makon jiya kwadayinsa ya jawo masa tozarta, kuma ina fata zai dauki lokaci yana auna irin kason yaudarar da jami’an gwamnati ke yi.
Wannan shi ne irin yanayin rayuwar mutane a Najeriya: wato rashin tsare mutunci. Kamar yadda na fada kan ministoci a lokacin, “daki ne mai munin shiga a lokacin da kowa ya san hakikanin yadda matsala take, kuma babu wanda yake da azamar gyara a kai. Wannan daki gidan wuta ne ba Tudun La’arafi.”
Baa bin mamaki ba ne da jirin ministocin da aka sallama bai kunshi na Ministan Man Fetur ba Misis
Diezani Allison-Maduekwe. Kuma bai kunshe da sunan Babban Lauyan Najeriya kuma Ministan Shari’a Mohammed Adoke Bello ba.  
Idan aka zo batun almundahana, ko shakka babu Allison-Madueke ce minister da ta fi fice a duniya. Kusan a kowane wata sai an yi zargin samun hannunta a keta wata doka ko ka’ida. Zargi ba daidai da tabbatar da laifi ba ne, amma kuma ba ya nufin mutumin na da gaskiya, wata hujjar da gwamnati mai amana ya kamata ta kula da ita. Kuma duk da haka, ko sau daya Gwamnatin Tarayya ba ta taba bincikar wani zargi da aka yi mata ba, ko don ta kunyata masu zargin ko ta tabbatar da gaskiyar Ministar. Sannan ko sau daya Ministar a kashin kanta ba ta taba mika takardar murabus ba, ko ta nuna wata damuwa kan mutuncinta.  
Haka lamarin yake ga Minista Bello, wanda ba ma an zarge shi da azurta kansa ta haram ba ne kawai, har da yadda yake tankwara Ma’aikatar Shari’a wajen aikata zalunci da barna. Nan ma gwamnati ko Minista Bello sun ki nuna cewa akwai babbar matsala lokacin da aka zargi babban lauyan gwamnatin da rashin da’a da aikata mugun laifi.
Akwai daure kai kan yadda wadannan mutum biyu suka zama ministoci mafiya karfi a Najeriya. Ba dayansu da yake da dabi’ar ya yi murabus. Ba wanda ya damu yak are mutuncin iyalinsa da yake amsa sunansu.
Iyalai: A baya iyalai suna alfahari su kare mutuncinsu. Ba za ka aikata abin da kaso a wajen gida ba, dole ka kare martaba da sunan iyalinka. Amma ban da yau. Iyaye ba su damu yaushe dansu zai kwaba kashi a dakin zamansu ba. Matukar dai akwai kudi masu yawa, maza ba su cika nuna wa matansu su tsare martabar aurensu ba. Mata ba su damu wace cuta mazajensu za su kawo gida ba, matukar an kunshe ta da takardun kudi.
Wannan shi ya sa ministocin Najeriya za su gwammace su mutu maimakon su yi murabus: Ba za mu iya lamuntar rashin zama a kan mulki ba, koda mun san ba za mu iya tabuka komai ba. Ba za mu iya zama ba mulki ba, koda ya bayyana abin da ake yi gagarumar yaudarar jama’a ne. ’Ya’ya ba su tambayar me ya sa ake kiran iyayensu da miyagun sunaye a jaridu ba.
Da manufar sauki ministocin tara na makon jiya an yi shi ne domin amfanin ’yan Najeriya, Allison-Madueke da Bello ne za su jagoranci jerin. Kuma idan za a yi batun kare mutunci da martaba, ministocin biyu ya kamata su yi murabus daga mukamansu tuntuni su mayar da hankali wajen kare martabarsu.
Bari in kammala da karin minista a gwamnatin: Ngozi Okonjo-Iweala, Ministar Kudi kuma Ko’odinetan Minista. Lokacin da na yi rubutu a wani wuri cewa ita ce mafi rauni a cikin dakin, na sha caccaka daga manyan masu sharhi, ciki har da wani abokina da ya bayyana kansa da dan jarida da ke zagayawa ofishinta da daddare.
Hujjata ba ta da sarkakiya: Ministar Mai Tagwan Mukamai rauninta ba na rashin shirya wa aikinta ba ne, na kira ta da mai rauni ne saboda ta zo ne a matsayin minister da ta fi dacewa ta ba da babbar gudunmawa, amma sai ta sarayar da wannan dama ta ci gaba da zama kan kujerarta a lokacin da Najeriya ta gaza tabukawa ta gaza cimma nasara ta gaza ci gaba.
Kuma sakamakon rashin irin wannan kare mutunci ne ya sa Oby Ezekwesili tsohuwar abokiyar aikin Okonjo-Iweala a gwamnatin Obasanjo da kuma Bankin Duniya ta fito ta kalubalanci martabar wannan gwamnati, inda ta yi kiran a zo a yi muhawara. Amsar Okonjo-Iweala: shiru. Kan zargin almundahana da ake wa Minista Allison-Madueke, amsar Okonjo-Iweala: shiru.
Wannan na nuna hudubar inganta tattalin arziki da ‘sake fasalin kasa’ da nuna gwamnati za ta samu nasara duk da rashin bin ka’ida a gwamnatin da kake ciki ba abu ne mai yiwuwa ba. Okonjo-Iweala ta fi kowa sanin samar da aiki da kokarin samar da aiki, sake fasalin kasa da shirin bunkasa kasa na 2010 za su zamo labarin kanzon kurege ne kawai idan lamarin ya zamo kamar na farin dango sun mamaye gona.
Batu ne na kare mutunci. Babbar matsalar Najeriya ita ce idan ba ka da karfin halin fuskantar muhimman matsaloli, ba wani abin damuwa kan abin da za ka iya yi, ko kake tunanin yi. Mutane irin su Usman da Okonjo-Iweala wajibi ne su rika tunanin makomarsu a tsanake, saboda wani lokaci kora kamar juyin juya-hali ne takan zo ne afke.
* [email protected]