Kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa (MSSN) reshen Jihar Legas sun yi kira ga gwamnatin Jihar da ta tabbatar da raba kwafin dokar tabbatar da sanya hijabi ga mata Musulmi a makarantun Jihar da Kotun Koli ta yi.
Shugaban kungiyar reshen Jihar, Malam Muftahudeen Thanni ne ya bayyana hakan a taron manema labarai ranar Laraba a Legas.
- ASUU: Saura kiris daliban jami’o’i su koma karatu – Gwamnatin Tarayya
- Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta tara N5bn a 2021
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a ranar Juma’a ce dai Kotun Kolin Najeriya ta ba mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantun gwamnati da ke fadin Jihar ,
Da yake taya kafatanin musulmin Jihar murna, Thanni ya ce wannan hukuncin ya kara tabbatar musu da ‘yancinsu na yin shiga daidai da tsarin addinin Musulinci, bayan shafe shekara 10 suna fafatawa a kotu kan kudirin.
Ya ce, “Yanzu abin da ya rage wa gwamnati shi ne gurfanar da bata-garin da ke da kunnen kashi daga malaman makarantar Jihar idan sun ki bin wannan dokar.
“Sai kuma batun raba kwafin dokar ga dukkan makarantun da ke karkashin ikon gwamnatin Jihar wata guda bayan zartar da dokar.
“Akwai kuma bukatar gwamnatin ta yi wani zaman tattaunawa da MSSN ta jihar, da jagororin Musulmi da sauran kungiyoyin addinin Musulinci kan girman hijabin da hanyoyin amfani da shi ga matan,” inji shi.
A karshe ya yaba wa alakalan da suka zartar da wannan doka, domin dakatar da abin da ya kwatanta da cin zarafi da kuma take Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.