✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mota dauke da tarakta ta kashe mace bayan danne tasi da take ciki a Abuja

Wata babbar mota ta dakon taraktoci ta yi ajalin wata fasinja da ke zaune a cikin motar tasi a Garin Nyanya Abuja. Lamarin wanda ya…

Wata babbar mota ta dakon taraktoci ta yi ajalin wata fasinja da ke zaune a cikin motar tasi a Garin Nyanya Abuja.

Lamarin wanda ya faru a safiyar Laraba nan da misalin karfe 11 kamar yadda wata majiya ta shaidawa Aminiya, ya auku ne a sanadiyar daukewar birkin motar wadda ke dauke da motar rusau.

Wani da lamarin ya faru a gabanshi mai suna malam Muhammad Sani, ya ce haka nan motar ta jikkata karin wasu mutane da ke cikin wasu motoci da ke tsaye a gefen hanya a lokacin da ta tinkaro ta wajen, kafin ta yi waigi da motar karshe da matar ke ciki tayi.

Ya ce, akwai kuma kamar motoci 8 da motar ta tagayyara ciki hadda wata kira gulf da ta rika turata kafin ta rabata gida biyu.

Bayanai sun ce, motar ta rasa birki ne, kuma tana samun damar tsayawa a wajen, sai direbarta ya taho da gudu.

Tuni dai jami’an kiyaye hadurra FRSC su ka garzaya da wadanda su ka tsira da raunukan zuwa asibiti, sannan aka janye motocin da suka tagayyaran daga wajen.