A wani yanayi na daban, na’urorin sadarwa da Hezbollah suke amfani da su, sun zama abubuwan fashewa.
Suna amfani da na’urorin ne domin guje wa fasahar Isra’ila na bibiyar su, amma sai suka rika fashewa a hannun mutane, har suka kashe wasu, suka kuma raunata wasu da dama.
- Matakan Tinubu na gyara kura-kuran gwamnatocin baya — Minista
- Tinubu ya umarci a taƙaita shagulgulan bikin Ranar ’Yancin Kai ta bana
Gwamnatin Lebanon ta zargi Isra’ila da harin, sannan Hezbollah ta ɗauki alwashin, “mayar da martani.”
Har yanzu Isra’ila ba ta ce komai a kan zargin ba, amma wasu kafafen watsa labarai a kasar sun ruwaito cewa, majalisar ministocin kasar ta hana ministoci magana a game da lamarin.
Isra’ila na bibiyar harkokin Hezbollah sosai, wanda hakan ke nufin watakila harin wani bangare ne na rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.
Idan har ta tabbata Isra’ila ce ta kai harin, zai zama ɗaya daga cikin salon yaƙi mafi ban mamaki da tasiri, wanda hakan ya sa aka fara waiwayen wasu hare-haren da kasar ta yi a baya da kuma tasirin hukumar leken asirin kasar wato Mossad.
Nasarorin Mossad
An sha yaba wa Mossad kan nasarorin da ta samu. Ga wasu daga cikin aikace-aikacenta:
Kama sojan Nazi Adolf Eichmann
Yadda Mossad ta shirya sato sojan Nazi Adolf Eichmann daga Ajantina a 1960 na cikin fitattun nasarorin da ta samu.
Eichmann, daya daga cikin wadanda suka jagoranci kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa, shi ne ya shirya yadda aka kashe Yahudawa a sansanin Nazi a lokacin Yakin Duniya na Biyu, inda aka kashe Yahudawa miliyan shida a Jamus.
Bayan guje-guje da ya yi a tsakanin kasashe, sai Eichmann ya tare a Ajantina.
Jami’an Mossad 14 suka rika bibiyarsa, har suka sato shi, sannan suka koma da shi Isra’ila, inda aka yi masa shari’a, aka yanke masa hukuncin kisa.
Aikin ceton mutanen jirgin Entebbe
Aikin ceton mutanen Entebbe da aka yi a Uganda ma na cikin nasarorin Mossad manya.
Mossad ce ta tattara bayanan sirrin, sannan sojojin Isra’ila suka dabbaka aikin.
Rundunar sojin Isra’ila ta Kwamando ce ta ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su a jirgin saman da ya taso daga Tel Aviv zuwa Paris ta Athens.
Jirgin yana dauke da fasinja 250, ciki har da ‘yan Isra’ila 103.
Wadanda suka kama jirgin – mambobin kungiyar fafutikar ‘yantar da Falasdinawa da taimakon wasu ‘yan Jamus – suka juyar da akalar jirgin zuwa Uganda.
Mutum uku ne suka mutu daga cikin wadanda aka tsare da wadanda suka kama jirgin da sojojin Uganda da dama da kuma Yonatan Netanyahu, wanda ƙani ne na Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a lokacin aikin ceto mutanen.
Ceto Yahudawa
A wani aiki na musamman mai cike da kwarewa, a shekarun 1980, Mossad – bisa umarnin Firaiminista Menachem Begin – ta kwaso sama da Yahudawan Ethiopia 7,000 ta cikin Sudan.
Sudan na cikin kasashen da suke tsama da Isra’ila, don haka shiga ta kasar zai yi wahala, amma sai jami’an Mossad suka bude wani wajen shakatawa a gabar tekun Sudan.
Da rana sai su rika aiki a matsayin ma’aikaten otel, da dare kuma su rika fitar da Yahudawan, wadanda suka tako a kafa tun daga Ethiopia, suna fitar da su.
Sai da aka yi shekara biyar ana wannan aikin, sannan a lokacin da aka gano jami’an Mossad din sun tsere.
Mayar da martani bayan garkuwa da mutane a gasar Olympics ta Munich
A shekarar 1972, wata kungiyar ‘yan bindiga ta Falasdinu mai suna Black September ta kashe ‘yan tawagar Olympic na Isra’ila guda biyu, sannan ta kama guda tara.
Daga baya aka kashe sauran wadanda aka kaman bayan ‘yan sandan Jamus sun gaza a aikin ceto su.
Daga baya Mossad ta mayar da martani a kan ‘yan kungiyar fafatikar ‘yantar da Falasdinawa, ciki har da Mahmoud Hamshari.
An kashe shi ta hanyar amfani da wani abin fashewa da aka dasa a wayarsa a gidansa da ke Paris.
A harin ne Hamshari ya rasa kafarsa, sannan daga baya ya rasu saboda raunuka da ya ji a harin.
Yahya Ayyash da fashewar wayar sadarwa
A wani aiki kamar wannan a shekarar 1996, an dasa giram 50 na abun fashewa a wayar Motorolla domin kashe Yahya Ayyash, wanda babban mai hada bom ne na Hamas.
Ayyash ya yi fice wajen hada bama-bamai da kai manyan hare-hare a Isra’ila, wanda hakan ya sa Isra’ila ta mayar da hankalinta sosai a kansa.
A karshen 2019, Isra’ila ta dage takunkumin bayyana wasu kashe-kashe da aka yi, wanda hakan ya sa tashar Channel 13 ta Isra’ila ta haska wayar karshe da Ayyash ya yi da mahaifinsa.
Yadda aka kashe Hamshari da Ayyash ya nuna yadda aka dade ana amfani da fasahar zamani wajen kisa.
Shake Mahmoud al-Mabhouh har ya mutu
A shekarar 2010, aka kashe Mahmoud al-Mabhouh, wanda babban sojan Hamas ne a otel a Dubai.
Da farko an yi zaton mutuwa ce ta Allah da Annabi, amma daga baya ‘yan sandan Dubai sun yi amfani da faifan bidiyon sirri wajen tabbatar da kashe shi aka yi.
Daga baya ‘yan sanda suka bayyana cewa, an saka masa shokin ne, sannan aka shake shi ya mutu.
An zargi jami’an Mossad da aikin, wanda ya haifar da sabanin diflomasiyya da Dubai.
Amma Ofishin Jakadancin Isra’ila ya ce, babu wata alama da ke nuna Mossad na da hannu.
Amma ba ta karyata lamarin ba, wanda dama yana cikin tsarin Isra’ila na raba kafa a irin wadannan al’amura.
Ayyukan da Mossad ba ta yi nasara ba Duk da nasarorin da ta samu, akwai kuma wuraren da ta yi rashin nasara.
Jagoran siyasar Hamas Khaled Meshal
Daya daga cikin ayyukan da suka jawo sabanin diflomasiyya mafi girma shi ne yunkurin Isra’ila na kashe Khalel Meshaal, Shugaban Siyasar Hamas a Jordan ta hanyar amfani da guba.
An samu tsaiko ne bayan an kama jami’an Isra’ila, wanda dole Isra’ila ta kawo makarin gubar domin a ceci rayuwarsa.
Jagoran Mossad na wancan lokacin, Danny Yatom ya shiga Jordan domin jinyar Meshaal.
Lamarin ya jawo sabani mai karfi tsakanin Jodan da Isra’ila Jagoran Hamas Mahmoud al-Zahar
A 2003, Isra’ila ta kai harin jirgin sama a gidan Jagoran Hamas, Mahmoud al-Zahar da ke Gaza.
Duk da cewa ya tsallake harin, an kashe matarsa da dansa, Khaled da wasu daban.
Lamarin Labon
A 1954, hukumomi a kasar Masar suka sanar da bankado aikin leken Isra’ila mai suna Susannah.
Wani yunkuri na samun damar dasa bama-bamai a kadarorin Amurka da Birtaniya a Masar domin tilasta wa Birtaniya ta ci gaba da jibge jami’anta a mashigar ta Suez.
Lamarin ne ake kira da Labon Affair, wanda aka sa masa sunan Ministan Tsaron Isra’ila, Pinhas Lavon, wanda ake tunanin shi ne ya shirya lamarin.
Yaƙin Yom Kippur
A ranar 6 ga Oktoban 1973, Masar da Syria sun kaddamar da hari a Isra’ila domin kwace yankin Sinai da Golan Heights.
Kaddamar da harin a ranar Yom Kippur, ranar da Yahudawa suke biki – ya shammaci kasar a farkon yakin.
Masar da Syria sun rika kai wa Isra’ila hare-hare a tare.
Dakarun Soviet Union sun taimaka wa Syria da Masar da makamai, ita kuma Amurka ta kai wa Isra’ila tallafin kayan agaji.
Isra’ila ta samu nasarar kawo karshen harin a ranar 25 ga Oktoba – kwana hudu bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a kawo karshen yakin.
Harin 7 ga Oktoban 2023
Kimanin shekara 50 baya, sai aka sake mamayar Isra’ila a wani harin daban, amma a wannan karon Hamas ce ta kaddamar da harin a garuruwan Isra’ila da ke kusa da Gaza a ranar 7 ga Oktoban 2023.
Yadda Mossad ta gaza gano shirin kai harin ba karamin cin fuska ba ne a wajenta, wanda masana suka nuna a matsayin gazawa.
Harin ranar 7 ga Oktoba ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 1,200, mafi yawansu fararen hula kamar yadda hukumomi a Isra’ila suka bayyana.
Sannan Hamas ta kama tare da tsare mutum 251 a Gaza.
Saboda mayar da martani a kan harin ne Isra’ila ta kaddamar da yaki a Zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 40,000, mafi yawansu fararen hula, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta bayyana.
Mun ciro labarin daga shafin BBC Hausa