✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Morata ya koma Chelsea

 Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararren xan qwallon gaban kulob xin Real Madrid na Sifen Alvaro Morata ya amince ya koma Chelsea na Ingila…

 Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararren xan qwallon gaban kulob xin Real Madrid na Sifen Alvaro Morata ya amince ya koma Chelsea na Ingila  bayan kulob xin ya amince ya saye shi a kan Fam Miliyan 68 kwatankwacin Naira Biliyan 27.

Xan qwallon xan kimanin shekara 25 tuni ya bar sansanin horar da ’yan qwallon Madrid da ke shirin tunkarar wasannin sada zumunta a Amurka inda ya koma Ingila don Likitocin kulob xin Chelsea su tabbatar da lafiyarsa kafin ya rattava hannu a kwantaragin.

Morata dai yana daga cikin ’yan qwallon Madrid da suka taimakawa kulob xin wajen lashe kofunan La-Liga da na Zakarun Kulob na Turai (Champions League) a kakar wasan da ta wuce amma koci Zinedine Zidane ya nuna xan qwallon bai yi masa ba.

Hakan ta sa xan qwallon ya nuna alamar barin kulob xin kuma yanzu da dama ta samu bai yi wata-wata ba wajen amincewa.

Idan ya sanya hannu a kwantaragin zai kafa tarihi a matsayin xan qwallo mafi tsada da kulob xin Chelsea ya tava sayo wa.

Kawo yanzu Chelsea ta sayi ’yan qwallo uku a shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta bana da suka haxa da Tiemone Bakayoko daga Monaco ta Faransa da xan qwallon bayan qasar Jamus Antonio Rudiger da kuma golan Ajantina Willy Caballero sai cikon na huxun Alvaro Morata da yanzu haka maganar cinikinsa ta yi qarfi.

Morata ya jefa qwallaye 15 a raga daga cikin wasanni 26 da ya buga wa kulob xin Real Madrid a kakar wasan da ta wuce.