✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyetti Allah ta zargi sojoji da kashe Fulani makiyaya biyu a Benuwai

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah  a Jihar Benuwai ta zargi sojoji da kashe mambobinta makiyaya  biyu a Unguwar Adeke, a garin Makurdi. Shugaban kungiyar…

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah  a Jihar Benuwai ta zargi sojoji da kashe mambobinta makiyaya  biyu a Unguwar Adeke, a garin Makurdi.

Shugaban kungiyar a jihar, Haruna Ibi ya bayyana cewa sun amso gawarwakin Fulanin biyu da aka kashe domin binne su, bayan da suka kai rahoton al’amarin ga ’yan sanda.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Ardon Otukpo, Risku Muhammad, ya ce Fulanin biyu da aka kashe suna daga cikin mambobin kungiyar a yankinsa. Ya ce a wajen karfe 12 na rana, Fulanin biyu suna tare da shanunsu, a lokacin da sojojin suka kashe su kuma suka kona gawarwakinsu.

Ta bangarensu, Kwamandan sojojin da ke sintiri a yankin, Filait-Laftana Abubakar Muhammad ya ce: “Na jagoranci ayarina muna sintiri a yankin a yau (Laraba), inda yayin da muke wannan sintiri sai muka hadu da makiyaya tare da shanu sama da 500. Suna ganinmu sai suka bude mana wuta, don haka sai muka mayar da martani kuma muka bar wurin.”

Babban Kwamandan Soja, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya ce, “Wannan shi ne irin kalubalen aikin da muke fuskanta a kullum, inda za ka ga makiyaya suna bude wa ayarinmu wuta. Idan su makiyayan sun kashe mu, babu mai jajanta mana kuma babu mai nuna wata damuwa ya saurari namu bangaren.”