✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Miyetti Allah ta yi tir da Gwamnatin Tarayya kan kisan makiyaya a Nasarawa

MACBAN ta yi zargin Gwamnatin Binuwai na da hannu cikin abin da ya faru.

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi Allah wadai da biris din da ta ce Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro sun yi dangane da kisan da aka yi wa Fulani makiyaya a Jihar Nasarawa kwanan nan.

Aminiya ta rawaito yadda a makon jiya jirgin yaki mara matuki ya sako wa wadanda lamarin ya shafa bama-bamai a kauyen Rukubi na Karamar Hukumar Doma, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 38.

Kungiyar ta ce duk da lamarin ya tayar da hankalin al’umma matuka, amma ko uffan mahukunta ba su ce a kai ba.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, Jami’in Hulda da Jama’a na MACBAN, Muhammad Nura Abdullahi, ya ce suna zargin akwai sa hannun Gwamnatin Jihar Binuwai cikin abin da ya faru.

A cewarsa, an bibiyi motar da ke dauke da shanu har ta kai inda ake da bukata kafin aka yi amfani da jirgin sama mara matuki ya sakar musu bam.

“MACBAN ta bayyana shirun a matsayin abin zargi da rashin la’akari da asarar rayukan talakawan Najeriya da suka fuskanci matsi daga gwamnatin Jihar Binuwai da jami’an rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ masu aiki daga Makurdi.

“Kungiyar na bukatar bayani dangane da kisan gangancin da aka yi wa sama da makiyaya da mahauta 40 a kauyen Rukubi cikin Karamar Hukumar Doma a ranar 25 ga Janairu, 2023.

“Makiyayan sun tafi Makurdi ne domin karbo shanu 1250 da Gwamnatin Binuwai ta kama musu bayan sun biya tarar Naira miliyan 29.

“Ko ba komai, mun sa ran jin Shugaban Kasa ya nuna alhininsa ga ’yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su.

“Wannan shi ne karo na uku cikin shekara guda da Sojojin Sama ke jefa wa makiyaya da dabbobi bam a jihohin Nasarawa da Binuwai da kuma Taraba,” in ji Abdullahi.