✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi ya koma kulob din Middlesbrough

Rahoton da kafar watsa labarai ta UK Sun ta Ingila ta kalato ya ce Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, John Obi Mikel…

Rahoton da kafar watsa labarai ta UK Sun ta Ingila ta kalato ya ce Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, John Obi Mikel ya koma kulob din Middlesbrough da ke Ingila, inda kulob din ya gabatar da shi ga magoya bayansa a shekaranjiya Laraba bayan kulla yarjejeniya da dan kwallon.

Obi wanda ya koma kulob din Tiajin Teda na China kimanin shekara biyu da suka wuce daga kulob din Chelsea, ya yanke shawarar sake komawa Ingila ne don ci gaba da kwallo bayan kwantaraginsa ta kare a China.

Kulob din Middlesbrough dai yana wasa ne a rukunin ’yan dagaji (Championship).  Sai dai ba a bayyana yawan kudi da kuma shekaru a yarjejeniyar da Obi ya kulla da kulob din ba.

Rahotanni sun nuna kafin Obi ya sake komawa Ingila kulob da dama ne suka yi zawarcinsa ciki har da Wolfsburg da ke Jamus da kuma Roma da ke Italiya.

Obi mai shekara 31, ya yanke shawarar komawa Ingila ce don ya taimaki Middlesbrough wajen sake haurawa gasar rukunin Firimiya.

Sai dai masana harkar kwallo suna ganin yin haka tamkar ci baya ne ga dan kwallon ganin yadda ya yi suna a fagen kwallo.  Sun ce kamata ya yi ya samu wani kulob da ke buga gasar Firimiya ta Ingila don ya farfado da martabarsa maimakon komawa rukunin ’yan dagaji.

Tuni Obi ya bayyana farin cikinsa game da komawarsa kulob din Middlesbrough inda ya sha alwashin taimaka wa kulob din wajen ganin ya sake komawa gasar Firimiya ta Ingila.