✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi ba zai halarci wasannin sada zumuntar da S/Eagles za ta yi ba

Kyaftin xin qungiyar qwallon qafa ta Super Eagles John Obi Mikel ya bayyana cewa ba zai halarci wasannin sada zumuntar da qungiyar qwallon qafa ta…

obi-mikelKyaftin xin qungiyar qwallon qafa ta Super Eagles John Obi Mikel ya bayyana cewa ba zai halarci wasannin sada zumuntar da qungiyar qwallon qafa ta Super Eagles za ta yi da qasashen Senegal da Burkina Faso a wannan wata da muke ciki ba.
Wasannin za su gudana ne a birnin London a wannan wata a shirye-shiryen tunkarar qasar Afirka ta Kudu a gasar neman hayewa cin kofin Afirka da kuma qasar Kamaru a gasar neman hayewa cin kofin duniya.
Xan shekara 29 Mikel Obi tuni ya aika wa Hukumar qwallon qafa ta qasa NFF wasiqar da ta nuna ba zai halarci waxannan wasanni na sada zumunta ba saboda waxansu dalilai da suka dabaibaye shi tun bayan da ya koma qasar Chaina da yin qwallo.
Xan qwallon ya nuna lokacin da aka sanya don yin wasannin sun ci karo da lokacin da za a fara gasar rukuni-rukuni na qasar Sin, kuma da wuya ya samu damar halartar wasannin. A shekaran jiya Laraba ne dai Jami’in hulxa da ’yan jarida na qungiyar Super Eagles Toyin Ibitoye ya sanar cewa Mikel ba zai samu damar halartar wasannin sada zumuntar ba.
Kocin Eagles Gernot Rohr dai zai yi amfani da wasannin sada zumuntar ne wajen zaqulo zaratan ’yan wasan da zai yi amfani da su a wasannin da qungiyar za ta yi da Afirka ta Kudu da kuma qasar Kamaru nan gaba kaxan.