Shahararren tsohon dan damben Boding Mike Tyson tare da shahrarrun ’yan kwallon Tennis da ke Amurka wato benus da Serena Willaism ana sa ran za su kawo ziyara Abuja don halartar bikin aza harsashin gina cibiyar horar da wasanni ta hadin gwiwa tsakanin Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da kuma John Fashanu da ake wa lakabi da Goodluck, Fashanu Inter Sports Academy.
Jakada Fashanu ne ya sanar da haka ga manema labarai a makon jiya a Abuja. Ya ce cibiyar za ta kasnace hadin gwiwa ce a tsakanin shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma John Fashanu, kuma za ta kasance ne a garin Abuja.
Ya ce gwamnati ta yanke shawarar kafa cibiyar ce don tallafawa matasa ta hanyar horar da su harkokin wasanni daban-daban da hakan zai rage zaman kashe wando kuma ya samar da ayyukan yi.
Ya ce tuni Ministan Babban Birnin Tarayya da ke Abuja Sanata Bala Muhammad ya amince da filin da za a gina cibiyar. Ya ce saboda haka ne aka fara shirye-shiryen gayyatar manyan baki musamman wadanda suka yi fice a bangarorin wasanni daga sassan duniya don su halarci bikin aza harsashin cibiyar a Abuja.
Ya ce tuni bakin da aka gayyata suka nuna aniyarsu ta halartar bikin da za a yi nan gaba kadan a Abuja.
“ Gwamnatin Najeriya ta amince da filin da a a gina cibiyar, kuma fili ne yalwatacce da babu irinsa a duk fadin Afirka”,
Tsohon dan kwallon Wimbledon da ke Ingila John Fashanu ya kara da cewa, baya ga Mike Tyson da benus da kuma Serena Williams, an gayyaci wasu daga cikin shahararrun ’yan wasa daga ciki da wajen Najeriya da suka hada da shahararren dan kwallon Najeriya Nwankwo Kanu da kuma shahararren dan tseren Birtaniya Linford Christie.
Ya ce ana sa ran kwararru ne za su rika horar da kowane sashe na wasanni a cibiyar idan aka kamalla ta.
Daga nan sai John Fashanu ya yi kira ga ’yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata don tallafawa cibiyar ta hanyar ba ba gudunmuwar kudi daidai gwargwadon hali.
“Kowa zia iya bayar da nasa gudunmawa daidai gwargwado ba sai masu hannu da shuni kawai ba.
“Ina kira ga daukacin ’yan kasa da su bayar da nasu gudunmuwa don ganin cibiyar ta samu nasara. Don haka duk mai niyyar bayar da taimako yana iya yin haka ta asusun cibiyar a bankin Zenith Bank mai lambobin ajiya kamar haka: 1004451687.
Idan aka kammala cibiyar za a rika horar da matasa harkokin wasanni daban-daban da suka hada da kwallon kafa da kwallon tenni da gudu da damben boding da kokawar turawa (wrestling) da tsalle-tsalle da kwallon kwando da badminton da sauransu.
Mike Tyson da Serena Williams za su ziyarci Abuja
Shahararren tsohon dan damben Boding Mike Tyson tare da shahrarrun ’yan kwallon Tennis da ke Amurka wato benus da Serena Willaism ana sa ran za…
