✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mika mulki daga PDP zuwa APC nasarar Dimokuradiyya- Namadi Sambo

A jawabin da ya yi, tsohon mataimakin shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo, da ya kasance shugaban taron, ya ce dawowar mulkin kasar nan daga hannun…

A jawabin da ya yi, tsohon mataimakin shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo, da ya kasance shugaban taron, ya ce dawowar mulkin kasar nan daga hannun jam’iyya mai mulki lokacin PDP zuwa ta APC da ke matsayin adawa a baya, babbar manuniya ce a kan irin matakin ci gaba da demokudiyya ta kai kasar nan.

Ya ce, tarihin demokuradiyyar ba zai cika ba, sai an hada da jajircewa da tsohon shugaban kasa Gooodluck Jonathan, ya yi na dagewa a kan samar da sahihin zabe ta hanyar nada tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, a matsayin shugaban na INEC, sannan ya taya abokin hamaryarsa shugaba Buhari akan nasarar zabe da ya samu, tun gabanin hukumar ta ayyana shi.