Lionel Messi ya sake kafa tarihi a ranar Asabar bayan ya ci wa kungiyar da yake buga wa wasa wato PSG kwallo a fafatawarsu da takwararta ta Nice a gasar Legue 1.
Hakan dai na nufin yanzu dan wasan dan asalin kasar Ajantina na da kwallo 702, kuma shi ne dan wasan da ke kan gaba a kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai, inda a yanzu ya wuce babban abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo, wanda ke da kwallo 701.
Messi ya sami nasarar ce duk da cewa yawan wasannin da ya buga sun gaza na Ronaldon da guda 105.
Ronaldo dai a yanzu shi ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya.
Kwallon da Messi ya zura a minti na 26 dai ita ce ta 14 tun da aka fara gasar. Kuma ya zuwa yanzu, shi ne dan wasan da ya fi kowanne yawan kwallaye a kakar wasa ta bana.
A lokacin da yake kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain, Messi mai shekara 35 ya ci mata kwallo 672 a cikin wasa 778 da ya buga mata.
Yanzu haka dai Messi ya buga wa PSG wasa 68 kuma a ciki ya ci mata kwallo 30.