✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mece ce shayarwa cikakkiya?

Yaya ta ce idan ta haihu da dan ya yi watanni shida da haihuwa sai ta yaye ta fara ba shi madarar formula da garin…

Yaya ta ce idan ta haihu da dan ya yi watanni shida da haihuwa sai ta yaye ta fara ba shi madarar formula da garin firiso.  A yanzu cikin na uku kenan. Ina so a yi bayani akan illar yaye a watanni shida.

 

Amsa: Lallai kuwa tana kuskure. Ko dai ba ta fahimci zancen da ake ta yi bane a baya game da shayarwa? Wato ko ta dauka muna cewa ne a shayar na wata shida a tsaya da shayarwa? Mu cewa muke a shayar da ruwan nono zalla (ba ruwa ba abinci) na watanni shida, sa’annan a ci-gaba da shayarwar a kuma fara ba da ruwa da abinci kamar kamu da sauran abinci masu taushi, da ‘ya’yan itatuwa masu ruwa da taushi har na tsawon a kalla shekaru biyu kafin a yaye. Wannan ita ce shayarwa cikakkiya. Sai dai kuma idan akwai wata larura ta lafiya da watakila ni da ke ba za mu sani ba, wadda ta sa likitanta ya ce iya watanni shida sun wadatar. Wasu mata da dama a yanzu a kasashen da suka ci-gaba suma sukan yi kuskuren yaye jariransu da sun yi wata shida, kawai saboda zamananci ba wai domin likita ya ce ba. Watakila itama wayewarce.

Ya kamata dai ta san cewa duk wasu alfanu da shayarwa za ta ba jariri kafin watanni shida suna ci-gaba da wanzuwa bayan watanni shidan, misali kariya daga kwayoyin cutuka, tunda a ruwan nono akwai kwayoyin garkuwa daga cutuka (antibodies) masu iya yakar kwayoyin cuta tun daga na mura zuwa na tari, zuwa na maleriya zuwa na gudawa, da uwa kan ci-gaba da ba danta, tunda jikinta ya riga ya san ciwon kuma ya sarrafa su. Akwai ma binciken da ya tabbatar cewa ‘ya’yan da aka shayar na tsawon yadda ya kamata ba su cika samun cutukan asma da borin jini ba. Banda wannan sai samun sinadaran abinci da suka dace da jariri, tunda jariri na girma abincin da ke cikin ruwan nonon ma na kara canzawa daidai da bukatunsa na wadannan watannin. Akwai kuma karin dankon soyayya tsakanin uwa da jariri. Wasu matan ma da yawa shayarwar kadai za ta iya hana su daukar wani juna biyun har sai ta yaye danta ya yi kwari.