✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mece ce alakar zazzabin Maleriya da Typhoid da ciwon Olsa?

Wai mece ce alakar zazzabin maleriya da na typhoid da kuma ciwon olsa. Domin idan mutum ya je asibiti a wannan aka auna shi sai…

Wai mece ce alakar zazzabin maleriya da na typhoid da kuma ciwon olsa. Domin idan mutum ya je asibiti a wannan aka auna shi sai a ce masa yana da biyu daga cikinsu ko su duka ukun.

Daga Saleh S. Ja’afar

 

Amsa: E, haka ne an fi ganin ciwon zazzabin maleriya da na typhoid a asibitocinmu saboda matsaloli na tsabta. Wato rashin tsabtar muhalli (wadda kan jawo maleriya) da rashin tsabtar abinci da abin sha (wadda kan jawo typhoid), shi ne babban abin da ke kawo wa harkokin lafiyarmu cikas a wannan kasa. Don haka da za a kiyaye wadannan tsabta kashi biyu da an daina ganin wadannan cutuka, tunda ai da akwai su a kasashe da dama, amma yanzu saboda cigaba, sai dai a irin kasashenmu kadai akan gan su.

Sai dai shi ciwon olsa ko gyambon ciki da kake cewa ana yawan samu da wuya ya kai yawan su wadannan zazzabi biyu na typhoid da maleriya.

 

Ni kuma matsalata ita ce a da hakorana reras suke, amma yanzu akwai wushirya tsakaninsu, shi ne na ke so a ba ni shawara.

Daga Ayuba I. Hadejia

 

Amsa: E, a asibitin hakori likitocin hakora a yanzu suna da dabarar yadda suke yi su cike wushirya, in dai ba ka so, tunda wasu kuma abin da suke sha’awa ke nan su yi wushirya. Amma dai in kana so a cike din ka tuntubi likitan hakori a babban birni ma fi kusa ke nan amma ba a Hadejia ba.

 

Ina shan ganyen shayi don na rage kiba amma ba na raguwa, shi ne na ke neman shawara

Daga Aisha Abbas

 

Amsa: To ban san dai inda kika gano cewa ganyen shayin da kika fada zai rage miki kiba ba. Muna sane da cewa akwai ganyayyakin shayi da dama da akan yi talla da sunan wai suna rage kiba. Amma dai a kimiyance rage yawan abinci da kayan ciye-ciye, da yawan motsa jiki a kullum, su ne hanyoyin rage kiba. Idan kuma irinsu teba ce kadai mutum ke da ita yake so ya rage, har da tiyata ma a yanzu akwai ta dame tebar.

 

Ni na kasance duk shekara sai na ba da jini amma kuma da an diba na yi ta ciwon kai ke nan. Ina mafita?

Daga A.B

 

Amsa: A’a to ga alama jinin kai ma bai ishe ka ba kake bayarwa. Duk da cewa akan yi gwaji a gani ko yawan jininka ya kai ka bayar, ba kasafai akan yi wannan gwaji ba, an fi yin na ajin jini a gani ko jininka wane aji ne, sai na kwayar kanjamau da hepatitis da ciwon hanta. Don haka yana da kyau a rika maka awo a ga yawan kwayoyin jininka sun kai ka bayar ko kuwa, kafin ka je a diba din, don kada wata rana a diba a zo ana cewa sai dai a mayar maka.

 

Na ci naman sallah da yawa yanzu tafukan kafata suna min zafi. Ga shi ina da ciwon suga. Mene ne abin yi?

Daga Ibrahim A., Makurdi

 

Amsa: E, ai dama yana daya daga cikin illolin yawan cin nama, wasu sinadarai da ake kira uric acid su taru a gabobi su rika kawo ciwo. Don haka abin yi shi ne a asibitin da kake karbar maganin suga za ka fada wa likitan a yi maka aune-aune a gani ko hakan ne ko wani abu ne daban.

 

Da gaske ne ruwan rijiya na da amfani ga jikin dan Adam?

Daga Junaidu Dutsinma

 

Amsa: E, ruwan rijiya mai zurfi kamar rufaffiyar rijiyar burtsatse ruwa ne mai kyau da mutum zai iya dauwama yana sha ba tare da wata matsala ba, domin rufin da zurfin yana hana kwayoyin cuta shiga rijiyar burtsatse, akasin wadda ba rufaffiya ko mai zurfi ba.

Idan kuma maganar kayan ma’adinai da sinadaran amfanin jiki kake da gaske ne ruwan zartsi ya fi na dadi wadannan sinadarai wadanda suke daidai yadda ba za su cutar da lafiya ba.

 

Mene ne illolin makaman nukiliya ga lafiyar dan Adam?

Daga Ibrahim Rabilu, Zamfara

 

Amsa: Makamin nukiliya kamar yadda sunan ya nuna makami ne na makamashi ba irin makami gama-gari da muka sani ba, kamar na kwari-da-baka ko harsashi ko takobi, wanda sai ya taba jikin kuru-kuru kafin ya yi illa. Shi makamin makamashi, wanda akan hada daga sinadarai da yawa, tun daga hydrogen, uranium, da plutonium da sauransu, makami ne mai illa ta hanyar tiriri mai zafi da cin nisan zango, wato ke nan ba sai ma ya taba dan Adam ba yake masa illa. In dai aka sake shi a kusa da inda wasu halittu suke, ko na dan Adam ko na dabbobi ko halittu na tsirrai, duk dai wani rai a kusa da wurin ka iya mutuwa. Nisan da aka lissafa karamin makamin zai iya kaiwa ya yi wa abu mai rai illa daga inda aka sake shi shine mil bakwai. Wato idan aka sake shi a wuri, duk wata halitta dake da’irar wurin har nisan mil bakwai za su iya mutuwa take. Wadanda suke wajen mil bakwai zuwa mil 10 za su iya konewa a fata ko su samu illa a kananan kwayoyin halittunsu na jini, ko su makance, ko dai su samu wata illa ta rashin lafiya.

Makaman nukiliya biyu ne kadai aka taba saki a inda mutane suke, wato a Hiroshima da Nagasaki a lokacin yakin duniya na biyu. Wadannan ma kanana ne domin na wannan zamani duk sun fi wadancan girma da illa da barna da nisan cin zango. Duk sauran makaman nukiliya da aka saki a duniya tun bayan wancan hari a tsibirai inda ba mutane ake sakinsu domin a yi gwaji. Sakamakon sakin makaman a wadancan birane an kiyasta cewa an rasa mutane kusan 200,000 sakamakon wannan hari, rabinsu a take suka mutu, sauran rabin kuma sanadiyar illar makamashin ce ta yi sanadinsu ba da dadewa ba. Wasu dubunnan daruruwan kuma haka suka gama rayuwarsu da tabon kunar harin, ko wata doguwar rashin lafiya mai alaka da harin.

To ka ji illolin makaman nukiliya.