✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me kuka ce Gizagawan Zumunci?

A wannan makon, kamar yadda muka saba daga lokaci zuwa lokaci, za mu mika filin ga Gizagawan Zumunci, domin su tofa albarkacin bakunansu. Bagizage Yusuf…

A wannan makon, kamar yadda muka saba daga lokaci zuwa lokaci, za mu mika filin ga Gizagawan Zumunci, domin su tofa albarkacin bakunansu.

Bagizage Yusuf A. Zamfara (GZG42ZMF) ne ya fara bude filin, inda ya yi korafi game da sukurkucewar al’amuran zumunci tsakanin Gizagawa. Daga bisani ya yi nasiha da jan hankali, domin mu dawo da zumuncinmu kamar yadda muka saba a baya. Ga abin da yake cewa:
“Assalamu alaikum, wannan budaddiyar wasika ce zuwa ga Gizagawa; da fatan kuna lafiya. Bayan haka, sanadiyyar wannan wasika tawa shi ne, ina cigiyar zumunci, wanda shi ne jigon Gizago, da ya bata tun bayan watanni da dama.
Rashin sa ya haifar da kasala, ganin laifin juna da rashin sanin halin da wasu suke ciki. Domin idan ba ku manta ba, a lokacin da yake nan ba mu da kasala a wurin kiran junanmu, wurin tura sakon gaisuwar Juma’a da ta jaje ko ta taya murna. Kuma a lokacin idan aka kira taro, ba mu yin kasa a gwiwa, har wani lokaci ma kafin a fara taron, za ka ji muna ta hira a tsakaninmu; sabanin yanzu da za ka ji kowa yi shiru sai can ka ji wani ya ce ‘kuna ji na?’
Daga karshe, ina rokon Gizagawa don Allah mu yafe wa juna duk wani abu da ke zukatanmu ko za mu iya gano inda zumunci ya boye.”
***
Kasancewar a dandalin Gizago na Facebook ne Malam Yusuf ya buga wasikarsa, nan da nan zaratan Gizagawa suka rika yi masa ta’aliki. Bagizage Suleman Idris ne ya fara ta’aliki, inda ya ce: “Allah Ya kara hada kanmu. Allah Ya kara mana son zumunci da kaunar juna.”
Baban Gobirawa kuwa sai ya buga kirarin Gizagawa, inda ya ce: “Gizagawa Zumunci! Zumunci Gizagawa!!”
Shi kuwa Umar Sa’idu dansadau, ga abin da yake cewa: “Hakika, Yusuf maganarka gaskiya ce kuma sai mun tashi tsaye domin gano inda ya nufa kuma wallahi duk shuwagabannin da suka bari zumuncin Gizago ya rushe ta sanadiyyarsu sai Allah Ya tambaye su; domin amana ce aka ba su. Allah Ya sa mu dace, amin.”
Hussaini Maikafet Aminin Aminiya sai ya amsa, ya ce: “Ka fadi gaskiya.”
Lawal Ambasada kuwa yana cewa: “Kai, gaishe ka Malam Yusuf, ka nuna kai cikakken Bagizage ne kuma kana rike da dalilin kafa wannan kungiya ta Gizagawa kuma Allah Ya saka da alheri; da fatan mun ji kuma za mu gyara.”
Shi kuwa Abdulkadir Prince cewa ya yi: “Da kyau, Allah Ya ba mu ikon gyarawa. Allah Ya ba da ladar fadakarwa.”
***
Shi kuwa Bagizage Sunusi Sani Dala, 08035800241 (GZG092NEJ), aiko da nasa sakon ya yin a daban, game da al’amuran mulkin Najeriya; ya bayyana takaicinsa yadda al’amura ke kara sukurkucewa. Ga abin day a tsokanta:
“Gizago, wai a ina gizo ke sakar ne? Malaman jami’a suna cikin wadanda ake nadawa ministoci, masu ba da shawara, masu hada sakamakon zabe da sauran mukamai amma ba mu taba jin wani ya ga an yi ba daidai ba ya ce ya ajiye aikinsa. Ana samun wasu cikin malaman addini da ’yan jarida suna son su ga an yi mulkin adalci amma idan an jawo su an ba su mukami sai ka ji shiru, kamar yadda wani ya ce ‘wa ya tsine wa Najeriya ne? Allah Ya kawo mana daukin gaggawa.”
To, Malam Sunusi, ai kai ma dan Najeriya ne, ya kamata ka san dalilin da ya sanya haka ke kasancewa. Inda gizo ke sakar dai shi ne, an bar turbar gaskiya, an jefar da duk wata kamala da ya kamata wajen tafiyar da al’amura. Al’ummarmu ta koma bautar kudi – iyaye suna son kudi, sarakunan gargajiya suna son kudi, ’yan siyasa suna son kudi, malaman addini suna son kudi, matasa maza da mata suna son kudi; to ta yaya al’amura za su tafi yadda ake so? Allah dai Ya kiyaye, amin. – Gizago!
***