✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke sa haqoran waxansu ke yin tsawo da girma cako-cako?

Shin me ke sa haqoran waxansu ke yin tsawo da girma cako-cako ta yadda ko sun rufe bakin haqoran ba za su rufu ba? Shin…

Shin me ke sa haqoran waxansu ke yin tsawo da girma cako-cako ta yadda ko sun rufe bakin haqoran ba za su rufu ba? Shin bambancin halitta ne ko ciwo ne?

 

Amsa: Wannan matsala da a likitance ake kira buck teeth wato haqoran zomo ba bambancin halitta ba ne ke kawo shi, ana ganin kamar ciwo ne, domin akwai wanda rashin wasu sinadarai na abinci ke sa wa, akwai kuma na rashin daidaituwar hava. Akwai ma wanda kan faru saboda yanayin abincin da yaro ya saba ci tun a quruciya, dangane da laushinsa ko taurinsa, domin yawan tauna abinci mai tauri yana daidaita qasusuwan hava inji masana.

Rashin sinadarai dalilansa kamar yadda ya nuna shi ne rashin wasu sinadarai a abinci na ma’adinai da na bitaman. Waxannan sinadarai da haqora ke buqata wajen girma da tsayuwa yadda ya kamata ana buqatarsu ne tun a yarinta lokacin da za a fara famfara da fiqa, domin su waxancan haqora na quruciya duk zubewa suke yi lokacin famfara komai muninsu komai kyawunsu. Ma’adinan da haqoran kuwa suke buqata sun haxa da fluoride (ana samu cikin ruwan sha da man makilin) da calcium (da akan samu a madara da kifi) da iodine (da akan samu a ruwan sha da gishiri) da zinc da phosphorous (waxanda ake samu a kayan lambu) da potassium (da akan samu a ayaba da sauran kayan itatuwa). Su kuma bitaman xin da haqora ke buqata kusan duka ne na A da B da C da D da E, su ma akan samu a abinci haxaxxe (wanda ya qunshi kowane aji na abinci) za a same su. To rashin samun irin wannan kayan sinadarai a abincin yaro zai iya sa wannan ciwo. Amma idan yaro har girmansa yana samun waxannan sinadarai a abinci sai ka ga da wuya ya samu haqoran zomo. Shi irin wannan nau’i na matsalar an fi ganinta a qauyuka inda ba a bai wa cimaka muhimmanci sosai.

Xaya nau’in kuma na rashin daidaiton hava kusan ba a matsalar abinci ba ne, a tsatso ne ko kuma a ce a qwayoyin gado ne wani zai gaji qwayoyin da za su sa havar ta yi qanqanta har a ga kamar haqora sun zazzago.

Ko ma dai mene ne sanadi a cikin waxannan matsaloli biyu da kan kawo zazzagowar haqora, akwai mafita. Zamani ya zo da cewa a yanzu irin wannan matsalar zazzagowar haqora kamar na zomo ana iya gyara ta. Idan haqoran ne kaxai da matsala, akan yi aiki a sa wayar qarfe a xaure a kuma matse haqoran har sai sun koma daidai kafin a warware ta, wannan tare da ba da magunguna ke nan da shawarwarin cin abinci masu waxancan sinadarai da za su sa kada a koma gidan jiya. Kai idan ma havar ce ke da matsala a yanzu akwai tiyatar gyara saitin havar. Don haka idan ka san mai irin wannan matsala za ka iya ba shi shawara ya nemi asibitin haqori gangariya domin a duba a ga ko zai iya morar irin wannan aiki.

 

Ni kuma ina da wani ciwo a dasashi. Sai ya tafi, sai ya dawo shi ne nake neman shawara.

Daga Rabilu Auwal Kano

Amsa: Eh ciwo a dasashi matsala ce babba wadda za ta iya tava lafiyar haqora. Matsala ce ke nan wadda lallai likitan haqori ya kamata ya duba ya ba da shawara.

 

Ni shekaruna ba su wuce 19 ba amma kullum barcina ba ya wuce awa uku a rana. Ko matsala ce wannan?

H. Musa, Kaduna

Amsa: Eh, wannan babbar matsala ce da za ta iya shafar lafiyar tunaninka da ta qwaqwalwarka da ta harkokinka kamar karatu ko ayyukanka na yau-da-kullum, saboda a shekarunka kamata ya yi aqalla ka riqa samun awa tara a rana kana barci. Don haka ke nan zama bai kama ka ba, sai ka je an binciki dalili a asibiti. Idan ma akwai wata hali kuma da ka sani kana yi da zai iya shafar barcinka kamar shaye-shaye ko da na shayi ne da kallon dare duk ya kamata ka bari kafin ka ga likita. Da fatan za a dace.

 

Ko me ke sa idan akwai farin wata na yi hira a waje sai na yi mura?

Daga Babangida Nafaxa, Gombe

Amsa: A tarihi da ilimin sanin halayyar xan Adam an yi rubuce-rubuce game da yadda farin wata ke tava lafiyar mutane, tun daga lafiyar qwaqwalwa zuwa mura har a lafiyar mata masu juna biyu, inda aka ba da misali da cewa wai mata sun fi shiga naquda idan akwai farin wata. A kimiyyance dai ba a tabbatar da haka ba in ban da cewa farin wata zai iya ragewa mutum awoyinsa na barci (wanda binciken kimiyya ya tabbatar).  Don haka ke nan mu a kimiyyance babu wani farin wata da ke sa mura sai dai idan an yi dace lokacin ya dace da yanayi na sanyi busasshe.

 

Ni kuma fitsarina ne ke warin maganin amfiklos. Ko matsala ce?

Daga Aminu Isa, Kano

Amsa: Ya danganta, domin a wasu lokuta abubuwan da muke ci na abinci ko na magani ta fitsari kaxai ake fitar da su, wasu kuma ta bayan gida kaxai, wasu kuma ta duka ba-hayar da fitsarin. Don haka idan a halin yanzu kana shan wannan magani, wanda da ma shi kusan kashi 90 cikin 100 a fitsari ake fitar da shi ba mamaki ka ji qamshinsa. Idan kuma ba ka ma sha maganin a ’yan kwanakin nan ba, to sai an yi maka gwajin fitsarin a gano me ke sa shi warin.

 

Wai da gaske ne duk wanda bai yi ciwon qarambau (ko farankama) ba a yarinta sai ya yi ko ya girma?

Daga Sani Umar Malumfashi

Amsa: A’a ba dole ba ne. Waxanda aka yi wa allurar rigakafin ciwon ai ka ga ba sa yin ciwon, saboda ita allurar wani nau’i ne na ciwon marar cutarwa ake xiga wa mutum don kada ya yi ciwon. Kuma mun tabbatar hakan na aiki domin in dai ba wai garkuwar mutum ce ta karye ba daga baya, duk wanda aka yi wa wannan allura da wuya ya yi ciwon har girma har mutuwa.