✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke jawo wahalar hadiya?

Da ina iya hadiye abubuwa kamar kwayoyin magunguna ba matsala, amma yanzu sai na marmasa su nake iya hadiyewa. Shin ko hakan akwai matsala ke…

Da ina iya hadiye abubuwa kamar kwayoyin magunguna ba matsala, amma yanzu sai na marmasa su nake iya hadiyewa. Shin ko hakan akwai matsala ke nan ga makogarona?

Daga Jamilu M. Adam

Amsa: Akwai dai wani ciwon makogaro da muka sani a likitance da ake kira achalasia, wanda ba kwayar magani kadai mutum yake shan wahalar hadiya ba, har lomar abinci ma tana wahalar wucewa. A wannan ciwo tun mutum na kasa hadiyar loma har ya zo abu mai ruwa-ruwa ma wahalar hadiya yake masa. To idan aka ga irin wannan tabbas ciwo ne, ba wai kwayoyin magunguna ba. Idan kwayoyin magunguna ne kadai ba ka samun matsalar hadiyar lomar tuwo to ba wata matsala, watakila kwayar ce ke razana ka.

Yadda ko lamarin shi wannan ciwo yake kuwa shi ne, a can kasan makoshi akwai wata tsoka mai budewa da rufewa a duk lokacin da aka sa mata abinci ko abin sha. To a wasu mutane wannan tsoka wata rana kawai sai ta kasa ko ta daina aiki, sai ka ga an ci abinci ya tsaya ya ki wucewa sai can an jima da kyar. Ana tunanin naman wurin na gajiya ne ko daina aiki haka kawai, ko don tsufa ko wani ciwon kari ko na daji da ya taba wannan tsoka. 

Ni ma idan na ci abinci sai na yi ta gamba. Ko me ke sa haka?

Daga Tajuddeen kaura-Namoda

Amsa: E, akwai wadansu mutane kalilan wadanda ke da irin wannan matsala ta cimakar dabbobi. Abin da muke kiran shi a likitance shi ne rumination syndrome, wato cimakar dabbobi. Haka kawai mutum zai ci abinci sai ya ji yana dawowa a baki sai an sake hadiyewa. Ba a san dalilin da ke kawo haka ba amma ana tunanin matsalar ba daga makoshi ko tumbin ciki take ba, daga kwakwalwa da tunani ne. Ana ganin masu irin wannan matsala sune za su yi maganinta ta hanyar yi wa cikinsu atisaye kamar na rike numfashi ko hakarkari daidai tumbin ciki bayan cin abinci ko a lokacin cin abinci domin kada lomar ta dawo, sai an tabbatar ta wuce kafin a saki.

Ni kuma dan kasuwa ne, sai na wayi gari a kwanakin nan duka abinda na yi a kasuwa to washegari ko zan mance shi; tun daga ciniki da wadanda na ba wa bashi da kudaden aljihuna, kai hatta kudaden kayan kasuwar lissafinsu na bace min. Shin wannan wane irin ciwo ne? Kuma wace shawara za a ba ni?

Daga Ibrahim A. Katsina

Amsa: E, tabbas wannan matsalar kwakwalwa ce da muke kira amnesia. Matsala ce da ke shafar kwakwalwa bangaren da ke ajiye bayanai na yau-da-kullum. Akwai abubuwa da dama da kan kawota kuma sun hada da buguwa a kwakwalwa bayan an yi wani hadari, akan iya samu ma bayan kwakwalwa ta kadu bayan samun wani babban tashin hankali kamar ganin kunar bakin wake kiri-da-muzu. Akwai ma rashin isassun bitaman na rukunin B1 wanda ake samu a hatsi, wadanda kwakwalwa da lakar jiki kan yi amfani da su wajen ayyukansu na yau-da-kullum. Matsalar tana ma iya faruwa ga masu ciwon farfadiya idan suka samu tashin ciwon, domin suma sukan mata wasu abubuwa da suka faru kafin tashin ciwon. Akwai ma wadansu abubuwan da sai dai binciken shi maras lafiyar ne kawai zai bayyana dalilin.

To tunda an ce matsalar kwakwalwa ce kenan sai ka nemi asibiti babba wanda suke da likitan kwakwalwa, wanda zai dubaka ya bukaci aune-aune da hotuna da sauran bincike domin gano musabbabi, kafin daga bisani a san irin maganin da za a rubuta maka. Kuma irin wannan matsala tana bukatar gaggawar bibiyar asibiti domin idan ba a gano musabbabin matsalar an yi maganinsa ba, matsalar na iya kara kamari.

Me ya sa idan na taba karfe wasu lokuta ko na yi musabiha da wani sai na ji kamar wuta ta ja ni?

Daga Muhammad A., Calabar

Amsa: A hannayen kowa akwai caji ko maganadiso na lantarki a lokuta daban-daban. Haka nan ma a jikin abubuwa kamar karfe da tufafi da sauransu akwai. Da yake lantarki ba ya zuwa sai an hada caji masu akasi wato positibe da negatibe, a mafi yawan lokuta ba akasin akan samu ba, wato akan samu positibe da positibe ko negatibe da negatibe, shi ya sa ba a jin shokin. Amma idan aka samu akasi tsakanin hannu da hannu yayin musabiha ko tsakanin hannu da karfe, to za a iya jin lantarki ‘yar kadan kamar shokin, amma ba wata matsala bace ko ciwo da za ka damu da shi.

Mene ne amfanin danyar gyada a jikin mutum? Idan babu wadanne matsaloli za ta iya sa wa?

Daga Tanimu Zangon-Buji

Amsa: Amfaninta daya da soyayya ko gasassa ko dafaffa sai dai danyar za ta iya zama kunshe da abubuwan da ba a so, kamar kwayoyin cuta da wata gubar acid da ake samu a gyada. Ita dafawar ko soyawar ne ke fitar da wadannan gubar da kwayoyin cutar.

Da gaske ne idan aka hada madara da ruwan kankara aka sha hakan zai iya maganin damuwa ko ciwon zuciya?

Daga Mukhtar Habib

Amsa: A’a wannan ba shi da asali a kimiyyance ko a likitance.

A ina ne za mu iya samun likitan hanci da makoshi a nan Katsina?

Daga Albada Ado

Amsa: Duk manyan asibitocinku biyu na Janara da FMC ba za su rasa bangaren da za a samu likitocin kunne da hanci da makoshi ba. Don haka wadannan za ka duba.

Ni ina yawan mura, kuma ina yawan shafa rabb da minsileta cikin hanci. Ko yin hakan na da matsala kuwa?

Daga Abubakar I., Abuja

Amsa: A’a ba wata matsala da aka san wadannan mayuka za su iya kawo maka.