✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ka sani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki? (1)

Marubuci: Stebe Dent, engadget.com Kusan shekaru dari da suka shude ne wata yarjejeniya kan kera motoci masu amfani da makamashin lantarki (Electric cars) ta ruguje…

Marubuci: Stebe Dent, engadget.com

Kusan shekaru dari da suka shude ne wata yarjejeniya kan kera motoci masu amfani da makamashin lantarki (Electric cars) ta ruguje tsakanin Henry Ford da Thomas Edison.  Babban dalili shi ne rashin ingancin fasahar batir mai iya taskance makamashin lantarki da zai ita tafiyar da motar.  Tun daga wancan lokaci motoci ke amfani da makamashin gas da fetur, wanda hakan ne ya jefa mu cikin zamani mai cike da dumamar yanayi.  Sai dai kuma, wani abin farin ciki shi ne a halin yanzu kamfanin Ford ya hada kai da kamfanonin kera motoci irin su Tesla da Chebrolet don kera motoci masu amfani da makamashin lantarki masu dimbin yawa.
Kamfanin Toyota ne ya jagoranci wannan sabon zamani, inda ya kera nau’in Prius mai amfani da makamashin gas da lantarki (Gas-Electric Hybrid).  A yayin da kamfanin Tesla ya samar da nau’in Elon Musk da Model S, wadanda ke amfani da zallan makamashin lantarki.  Nau’ukan motoci masu amfani da makamashin gas da lantarki su suka fi shahara, duk da bambancin da ke tsakaninsu.  Misali, nau’in Toyota Prius ta sha bamban nesa ba kusa ba da nau’in bolt na kamfanin Cheby; duk da cewa dukkansu suna amfani da makamashin gas da lantarki ne.  To me ya sa ake samun wannan bambacin fasaha waje kerawa?  Bari mu kutsa duniyar sababbin nau’ukan da aka kera masu amfani da ko dai makamashin lantarki zalla ko na lantarki da makamashin gas, mu gani.

Me ye Haka Kuma?
Tarihin motoci masu amfani da makamashin lantarki ya faro ne daga farkon shekarar 1880, amma wacce aka kera ta hakika a farko, ita ce wadda hamshakin mai kudin Ingilan nan wato Thomas Parker ya kera a shekarar 1884.  Fasahar motoci masu amfani da makamashin ta kasaita iya gwargwado a karni na 19, musamman cikin shekarar 1912, sadda aka kera wajen 34,000 a Amurka kadai.  Wannan adadi kusan shi ne  adadin nau’ukan masu amfani da lantarki da gas da aka kera a shekarar 2002.  Ire-iren wadannan nau’ukan motoci na nan birjik a cikin birane suna shawagi, saboda saukin mu’amalarsu.  kari a kan haka, motoci ne da aka yi masu cin gajeren zango, kuma galibin masu saye da hawansu mata ne.  Amma bayan ci gaba da aka samu wajen inganta tituna da kuma ma’adanar man fetur mai dimbin yawa da aka gano, sai motoci masu amfani da man fetur suka yawaita fiye da masu amfani da lantarki da gas.  Zuwa tsakiyar shekarar 1910 sai galibin kamfanoni suka daina kera motoci masu amfani da makamashin lantarki tsantsa, sai ‘yan kadan hana rantsuwa da suka ci gaba da kera kananan motoci na musamman da ake amfani da su wajen dauko abubuwa a filayen kwallon gof ko wuraren gine-ginen gidaje.
Daga nan aka daina kera ire-iren wakannan motoci, in ka debe wani gajeren yunkuri da aka yi wajen kera nau’in Henney Kilowatt tsakanin shekarar 1959 da 1960, wacce ba ta yi kasuwa ba a karshe.  An ci gaba da gudanar da bincike don fadada wannan fasaha ta nau’in abin hawa, har zuwa shekarar 1967 lokacin da aka kera nau’in Amitron da kamfanin American Motors ya kera.  Wannan nau’in mota mai amfani da hadakar makamashin lantarki da gas ita ce kuma nau’in farko har wa yau da aka kera wadda ke iya rage karfin makamashin lantarki a duk sadda aka taka birki, don baiwa na’urar rike makamakin motar damar alkinta makamashin da ke cikinta.  Wannan yasa motar ke iya daukar dogon zango sanadiyyar maimaituwar karfi da makamashinta ke samu a duk sadda aka taka birki.  An ci gaba da amfani da wannan dabara na fasahar Amitron a nau’ukan motocin kamfanin Audi da bolbo da ma wasunsu da dama. (Zan ci gaba mako mai zuwa)