Duk shugaban da yake son kwatanta adalci, to yana bukatar koyi da daukar darussa daga rayuwar Umarul Faruk. Ba wai ungulu da kan zabo ba, wato a fake da adalcin Umarul Faruk, a yi ta tafka ta’asa da handama da babakere ba. A yi amfani da doka, a kwashe kudaden talakawa da sunan kyautata wa shugabanni ko wakilai na kan mulki da wadanda suka sauka, ta hanyar gina musu gidaje da ba su motoci da kudaden sharholiya, duk daga dukiyar talakawa.
Daga cikin darussan adalci daga rayuwar Umarul Faruk (R.A) akwai:
1. Umarul Faruku ya kasance yakan sanya wa gwamnonin lokacinsa ka’idar irin rayuwar da ya kamata su yi; ta yadda ba za su fifita kansu a abin hawa ko abinci ko kuma tufafi a kan sauran jama’a ba. Haka kuma yakan hori kowane Gwamna ya bar kofar ofishinsa a bude, domin karbar nasiha ko shawara ko korafi ko kuma koke-koke. Saboda haka a duk lokacin aiki Hajji yakan bi shemomi, yana tambayar talakawa halayyar gwamnoninsu.
A irin wannan kewaye da yake yi ne, ya je ga mutanen Hims (Siriya) ya tambaye su: “Yaya kuke? Kuma yaya gwamnanku?” Sai mutanen Hims suka ba shi amsa cewa: “Ai gwamnanmu ya fi duk sauran gwamnoni ya Amirul Muminina. Sai dai ya gina wani wurin da, in ya shiga ba ya sauraren kowa.” Jin haka sai Amirul Muninina ya rubuta masa wasika, ya aika wasika tare da jakada, kuma ya ba shi umarnin, in ya isa Hims, ya zarce kai-tsaye wannan ofis din da Gwamnan ya gina, ya tara itace ya kone kofar. Da jakadan ya je, sai ya aikata kamar yadda Amirul Muminina ya umarce shi. Ganin haka sai wasu suka yi gaggawa, shi kuma Gwamnan ya ce: ‘Ku kyale shi, Jakadan Amirul Muminina ne. Sai jakadan ya shiga ya mika wa Gwamnan wasikar Amirul muminina. Nan da nan Gwamnan ya tashi ya nufi Madina. Da Amirul Muminina ya hango shi, sai ya bayar da umarni a je a tsare shi a kurkuku a rana, har tsawon kwana uku. Bayan ya gama kwanaki ukun, sai aka kawo shi gaban Amirul Muminina, wanda nan take ya ce a tafi da shi turken dabbobin zakka ko sadaka na Al-Harah, a inda ya ba shi bokiti ya umarce shi ya shayar da dukkan dabbobin nan ruwa. Sai da ya yi tikis saboda gajiya, kafin ya gama shayar da dabbobin nan. Bayan ya gaji aka dawo da shi wurin Amirul Muminina ya tambaye shi: “Tun yaushe kake Gwamna a Hims? Sai ya ce: “Na dauki tsawon lokaci ya Amirul Muminina. Sai Amirul Miminina ya ce: Shi ne dalilin da ya sanya ka gina wa kanka wani wuri (don ka guji jama’ar da kake shugabanta), don tozartar da raunanan Musulmi da marayu da kuma zawarawa da sauransu? Ka koma ka ci gaba da shugabacinka na Gwamna, amma kada ka kuskura ka sake yin laifin da har sai na neme ka.” (Arriyadun Nadirah).
Wannan shi ne tsantsar adalci. Shi fa wannan Gwamnan bai zalunci kowa ba. Laifinsa kawai nesanta kansa da jama’a, ba tare da gamsar da jama’ar a bisa dalilin yin hakan ba. Wannan shi ne kawai dalilin da ya sanya ya fuskanci horon Amirul Muminina. Don haka shugaba ya rika yin kuka ko Allah Ya isa kawai, ba siffar adalci ba ne. Wani salo ne kawai na zalunci da yaudara da kuma cin amanar al’umma da shugabanci.
2. Wata rana Usman dan Affan (RA) yana gudanar da kasuwancinsa a wani wuri da ake ce masa Al-Aliyah a lokacin tsananin zafin ranar Sahara, sai ya hango wani mutum janye da rakuma biyu manya. A wannan lokacin, kai ka ce yashin sahara birbishin wuta ne (saboda tsananin zafi). Sayyidina Usman dan Affan (RA) ya yi mamakin ganin wani a irin wannan lokaci, har ma sai da ya ce “Ai wannan mutumin kamata ya yi ya zauna a gari, har sai yanayi ya sanyaya, sannan ya fito wannan tafiya tasa. Wani hadimin Sayyiduna Usman ya ce, “Ka san kuwa ko wane ne wancan din?” Da Sayyiduna Usman ya dada dubawa, sai ya ce: Ni dai na fahimci wani mutum ne da ya lullube kansa da mayafi, yana janye da rakuma biyu. Shi ne sai hadimin ya ce: “Ka dai dada dubawa sosai!” Yana sake dubawa a tsanake, sai ya gane ashe Amirul Muminina Umar bin Khaddabi ne. Nan take cikin mamaki ya ce: “Ai Amirul Muminina ne! Nan da nan ya mike tsaye ya je ya bude kofar shemar da yake ciki, amma hucin turirin zafin sahara ya sanya ya kasa fita. Da Amirul Muminina Umar bin Khaddabi ya karaso inda suke, sai Sayyiduna Usman ya tambaye shi. “Ya Amirul Muminina me ya fito da kai a yanzu haka?” Amirul Muminina Umar bin Khaddabi ya ba shi amsa cewa: “Wasu rakuma biyu ne na Baitul-mali aka bar su baya, alhali sauran rakuman sun yi gaba. Ina kokarin na riski wadancan ne a wurin kiwonsu na hada su. Domin in har suka bata, to, sai Allah Ya tuhume ni a game da su a gobe kiyama. Sayyiduna Usman ya ce: “Ya Amirul Muminina! Zauna a nan ka dan sha ruwa ka huta, mu za mu aiwatar da wannan aikin, shi ne sai Amirul Muminina ya ba shi amsa da cewa: “Koma ka ci gaba da hutawarka ya Usman” sannan ya zarce abinsa. A nan ne Sayyidina Usman ya ce: “Duk wanda yake son idanuwansa su ga jajirtaccen adalin shugaba kuma mai gaskiya, to ya kalli Umar.”
Wannan ita ce dabi’a ta shugaba mai adalci. Wato rayuwarsa hidima ce ga al’umma da addini, tare da tunanin yadda zai hadu da Allah Ta’ala lafiya, a game da amanar mulkin da Allah Ya jarrabce shi da shi. Wannan ya saba da yadda ake gudanar da mulki ko shugabanci ko wakilci ko kuma jagoranci a yau a wannan nahiya tamu, inda masu mulki ke gudunar da shugabancinsu kamar wasu dabbobi ko bayi suke mulka. Kai ma gwanda dabba a kasar nan. Dabba ana ba ta abinci da ruwa da gyara mata wurin kwana saboda kada ruwan sama ya same ta.
3 Abdullahi dan Umar (RA) ya bayar da labarin cewa: “Wata rana na sayo rakuma ramammu, sai na kai su inda rakuman Baitul- Mali da na sauran jama’a ke kiwo. Bayan da suka koshi, suka zama manya bul-bul, sai na je na kwaso rakumana, na kai su kasuwa. Wata rana Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (RA) ya shiga kasuwa rangadi, sai ya ga kosassun rakuman, sai ya tambaya, “Wadancan rakuman na wane ne?” Sai aka ce masa: “Na Abdullahi dan Umar ne.” Da muka hadu da shi, sai ya ce mini: “Ya Abdullahi! Ka kyauta! Ka kyauta! dan Amirul Muminina! Jin haka sai na je wurinsa da gaggawa na tambaye shi: “Me ya faru?” Sai ya tambaye ni game da rakuman nan. Sai na ba shi amsa cewa: “Wasu ramammun rakuma na sayo a kasuwa, shi ne na kai su inda rakuman jama’a ke kiwo. Sai Umar (RA) ya ce wato jama’a suka yi ta ba su abinci da ruwa, suna cewa rakuman dan Amirul Muminina ne, ku ba su abinci da ruwa ko, shi ya sa suka yi bul-bul suka fi na kowa girma da kiba. Take Amirul Muminina ya ce, “To ka sayar da su, ka dauki asalin kudinka da ka sayo rammamun nan, sauran kudin ka kai a zuba su a Baitul-malin al’umma.” Tirkashi! Aiki sai mai shi! Duba saboda cikar adalci, yadda Amirul Muminina ya toshe kofar amfani da duk wata dangantaka don a fake a azurta kai
Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08060116666, 08023106666
Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (4)
Duk shugaban da yake son kwatanta adalci, to yana bukatar koyi da daukar darussa daga rayuwar Umarul Faruk. Ba wai ungulu da kan zabo ba,…