✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (3)

Dalilan adalci a Sunnah:Kamar yadda ayoyi da dama suka yi magana a kan adalci, to haka ma akwai Hadisai birjik, da suke bayani a game…

Dalilan adalci a Sunnah:
Kamar yadda ayoyi da dama suka yi magana a kan adalci, to haka ma akwai Hadisai birjik, da suke bayani a game da adalci da adalai. Wato matsayinsu da kuma falalarsu. Daga cikin wadannan Hadisai akwai:
1. “Adalci kyakkyawan dabi’a ne, amma ga shugabanni ta fi kyautatuwa. Kyauta kyakkyawar dabi’a ce, amma ga mawadata ta fi kyautatuwa. Tsantseni kyakkyawar dabi’a ce, amma ga malamai ya fi kyautatuwa. Hakuri kyakkyawar dabi’a ce, amma ga talakawa ya fi kyautatuwa.
Tuba kyakkyawar dabi’a ce, amma ga matasa ta fi kyautatuwa! Kunya kyakkyawar dabi’a ce, amma ga mata ta fi kyautatuwa.” (Dailami ne ya ruwaito shi, daga Umar Ibnu Khaddab).
Wannan Hadisi yana bayyana cewa shugabanni ne suka fi   cancantar su yi adalci, fiye da sauran al’umma. Domin su adalcinsu kan iya amfanar kowa da komai, kamar yadda zaluncisu ke iya cutar da kowa da komai. Annabin Rahma (SAW) ya ce: “Dukkanku jagorori ne, kuma kowannenku sai an tambaye shi a game da jagorancin da yake kansa.” Wato wannan shugabanci ya hada da malamai da Shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da ’yan Majalisar Tarayya da na jihohi da kansiloli da kwararru da sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwanni da sakatarori da ma’aji-ma’aji da masinjoji da kuku-kuku da masu gadi da sauran wakilan zartarwa da gudanarwa da alkalai da rajistarori da ’yan aiken alkalai da lauyoyi da masu gida da matan aure da hadimai da leburori da attajirai da wakilan sabgogi da duk wani wanda yake da damar ya gudanar da wani lamari, ko zartar da shi, ko kuma bayar da shawara. Wato kowane daga cikin wadannan mutane wajibi ne a gare shi ya yi adalci, saboda damar da yake da ita, na yiwuwar wani lamari, ko rashin yiwuwarsa, ko kuma yiwuwarsa yadda ya kamata.    
2. “Lallai masu adalci za su kasance a kan mumbarin haske a wurin Ubangiji (wato a gobe kiyama). Su ne wadanda suke adalci a shugabancinsu ko hukuncinsu da iyalansu da kuma duk wanda suke jibintar lamarinsu.” (Muslim ne ya ruwaito shi; daga Abdullahi dan Amru dan Ass).
Wannan Hadisi yana nuna matsayin adalan shugabanni da adalan alkalai da adalan iyaye da adalan masu jibintar lamuran al’umma a dukkan fannonin rayuwa da addini. Wato za su kasance a wurare na alfarma, kuma za su kasance a kan karagu na haske, saboda matsayinsu da darajarsu da kuma alfarmarsu a wurin Allah Ta’ala a gobe kiyama.
3. “Mutum bakwai, Allah zai sanya su a inuwar Al’arshinSa, a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali. Da saurayin da ya taso cikin bautar Allah. Da mutumin da a koda yaushe yake ta’allake da masallaci. Da mutum biyu da suke kaunar junansu domin Allah, wato in ka gan su tare kaunar Allah ne ya hada su, in kuma sun rabu, to saboda Allah suka rabu. Da mutumin da mace mai daraja kuma kyakkyawa, ta neme shi da zina ya ce: “Ni ina jin tsoron saba wa Allah.” Da mutumin da yake yin sadaka da dama, amma hagunsa bai sani ba. Da kuma mutumin da yake tuna Ubangiji a boye, har idanuwansa su rika zubar da hawaye.”  (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi, daga Abu Huraira (R.A).
Wannan Hadisi yana bayyana irin matsayin adalin shugaba a gobe kiyama. A lokacin da kowa ke cewa NAFSI-NAFSI (ta-kaina-ta-kaina), saboda tsananin masifa, amma shi a wannan rana yana daga cikin wadanda za su fake a inuwar Al’arshin Allah Madaukaki. Kuma shi ne na farko da Annabi (SAW) ya ambata a jerin wadanda za su kasance a inuwar ta Al’arshi.
4. “Ma’abuta Aljanna mutum uku ne: Ma’abucin mulki da ya yi adalci a cikin gaskiya (shiriya), da mutum mai tausayi da tausasawa ga duk makusancinsa (’yan uwa da iyalai da hadimai da sauran abokan hulda), da kuma sauran Musulmi. Da ma’abucin iyali mai kamewa da taka-tsantsan (a game da neman dukiya).” (Muslim ne ya ruwaito daga Iyad dan Himar).
Wannan Hadisi na bayyana cewa adalci kan iya kai mutum ga samun aljannar Allah da rahamarSa. Amma sai in mutum ya yi adalci, kamar yadda Allah da Manzo (SAW) suka bayyana, ba wai adalcin molon-ka ba, ba tare da wata hujja daga shari’a ba. Don haka duk adalcin da ya saba wa shari’a, to shi ma nau’in wani zalunci ne.
5. “Mafifitan shugabanninku, su ne wadanda kuke kaunarsu, su ma suke kaunarku. Kuna yi musu addu’ar (alheri), su ma suna yi muku addu’ar (albarka). Kuma ashararan shugabanninku su ne wadanda kuke kinsu, su ma suke kinku. Sannan kuke la’antar su, kuma su ma suke la’antarku. Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah! Shin ba ma yi watsi da su (ashararan shugabannin) ba?” Sai Manzon Allah ya ce: “A’a! Matukar suna tsayar da Sallah a cikinku.” (Muslim ne ya ruwaito daga Aufu dan Malik).
Wannan Hadisi yana bayyana alamomin adalan shugabanni, wato su ne suke aiwatar da abubuwan da al’umma ke gamsuwa da salon shugabancinsu, don haka suke kaunarsu. Wato suna gudanar da ayyukan raya kasa da tallafi da bunkasa addini da kyautata zamantakewa da inganta tattalin arzikin jama’a da kuma kulawa da raunana ko talakawa ko marasa lafiya da sauran nakasassu da mabukata. Tabbas shugabannnin da suka tsayu da irin wadannan ayyuka, suna kaunar jama’arsu. A dunkule dai shugabannin nan suna kulawa da kyautata addini da tattali arziki da nasaba da mutunci da kuma rayuwar al’umma. Haka kuma suna da gaskiya da amana da alkawari a bisa gudanar da shugabancinsu. Sannan su kasance ba su da kwauro ko almubazzaranci. Bugu da kari, ba sa zaluntar al’umma, kuma ba sa barin wani ya zalunce su da kowane nau’in zalunci. Wannan rashin zaluncin da kuma hana zalunci da suke yi, shi yake sanya al’umma su kaunace su. Idan al’umma suna kaunar shugabanninsu, to sukan yi musu biyayya, tare da kyautata musu zato da kuma yi musu fata da addu’o’i na alheri.
Idan kuma aka samu akasin haka, wato shugabanni suka kasance ashararai, masu watanda da dukiyar talakawa da rusa tattalin arzikin al’umma da tozarta musu addininsu da rusa musu martabar zamantakewarsu da raunana musu harkoki lafiya da na ilimi da kassara musu zaman lafiya da nutsuwarsu, to irin wadannan shugabanni babu abin da zai faru a tsakaninsu da wadanda suke mulka, sai tsine-tsine da munanan zato. Musamman ma idan ya zama shugabannin jahilai ne ko kafirai ko ja’irai ko munafikai ko fasikai ko kuma masu girman kai ne.
Umarul Faruku: Samfurin adalci:
Babu wani shugaba da zai iya adalci irin na Annabin Rahma (SAW), kai babu ma wanda zai iya kwatanta adalcin sahabbansa, musamman irin jan-gwarzo Amirul Muminina Umarul Faruk bin Khaddabi (RA). Kai hatta ma a cikin sahabban, yana da wuya a samu kamar Umar dan Khaddabi. Shi ne shugaban da ya zarce wadanda suka gaba ce shi, sannan ya gajiyar da wadanda suka zo a bayansa, in dai ana maganar adalci a shugabanci. Saboda haka Musulmi da wanda ba Musulmi ba, suka sallama masa.
Abdulkarim daiyabu,
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08023106666, 08060116666