✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayar da kayan zalunci ne tushen adalci (2)

Shugabanni da masana da mawadata da kuma kwararru na fannoni dabam-daban su ne manyan turakun da ke rike kowace al’umma. Wato idan al’umma ta lalace,…

Shugabanni da masana da mawadata da kuma kwararru na fannoni dabam-daban su ne manyan turakun da ke rike kowace al’umma. Wato idan al’umma ta lalace, to wadannan su ne suka gurbace. Haka kuma idan al’umma ta gyaru, to, su nagartattu ne. Kamar yadda Sallah ba za ta inganta ba, sai da alwala, kuma tuba ba zai inganta ba, sai an yi nadama. Haka kuma adalci ba zai taba tabbata ba, sai shugabanni da alkalai sun mayar wa wadanda aka zalunta hakkokinsu.
Wanda ya musulunta ne kawai, shari’a ta yafe masa duk abin da ya gabatar, na barna kafin ya shiga Musulunci. Amma wanda yake ciki Musuluncin, matukar akwai dalilin zargi a tare da shi; to shari’a ta yarda a yi bincike domin kare wannan zargi ko kuma tabbatar da shi. Idan kuwa har zargin ya tabbata, kuma akwai hakkin al’umma ko hakkin wani, to a nan Raddul Mazalimu ta wajaba: wato mayar wa wanda aka zalunta hakkinsa. Ko kuma shari’a ta daukar masa fansar zaluntarsa da aka yi. Da kuma toshe kafar yiwuwar yin wani zaluncin a nan gaba.
Zalunci shi ne kishiyar  adalci, kuma ba za a iya fahimtar mene ne zalunci ba, sai an san mene ne adalci.
Ma’anar adalci a kur’ani:
Allah Subhanahu Wa Ta’ala, Ya yi bayani a game da adalci a wurare da dama a cikin Alkur’ani. Muhimmai daga cikin wadannan ayoyi su ne:
1.    “Lallai Allah Yana umartar ku, da ku mayar da amanoni ga ma’abotansu. Idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to, ku yi hukunci da adalci ….” (Suratul Nisa’i:58).
Wannan aya tana nuni ga umarnin Allah game da bayar da shugabanci ko wakilci ko jagoranci ko amanar al’umma ko amanar kudi ko amanar kaya  ko wata ajiya ko kuma amanar kowane alkawari ga wadanda suka cancance shi a shari’ance ko a mu’amalance ko a ilimance ko a kwarance ko kuma a ka’idance.
Don haka jahilan lamari ko maha’inta ko mutane marasa nagartar hali ko rashin nagartar asali ko wadanda ake tuhuma da zalunci ko almubazzaranci ko kwauro ko rowa ko keta ko kuma tsananin kwadayi, sam ba su cancanci shugabanci ko wakilcin al’umma ba. Haka kuma wannan aya tana umarni da yin adalci a cikin duk wata sabga ta hukunci, wato shugabanni da wakilai da alkalai da sauran jagororin al’umma su kasance mutane ne adalai, a bisa yadda suke gudanar da dukkan lamuransu na al’umma.
2.     “Kuma idan za ku yi magana, to, ku yi aldalci, koda kuwa a kan ma’abocin kusanci ne ….” (Suratul An’am:152).
Wannan ayar tana umarni ne da fadin gaskiya da daidaito a kan kowane lamari, koda kuwa bayyana gaskiyar za ta nuna illar makusanci, kamar dan uwa ko makwabci ko aboki ko duk wani makusanci, koda kuwa mahaifi ne ko mahaifiya ko ’ya’yan mutum, matukar bayanin shi ne zai samar da maslaha ko gyara ko warware matsala ko kuma gusar da barna.
3.     “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa ga umarnin Allah ta hanyar yin shaida ta adalci. Kada kiyayya da mutane ta hana ku yi musu adalci.  Ku yi adalci shi ne mafi kusanci ga tsoron Allah ….” (Suratul Ma’ida:8).
Ita kuma wannan ayar tana umarni da yin shaida ta adalci a bisa kowane mutum, Musulmi ne ko kafiri ne, mutumin kirki ne ko mutumin  banza ne, dan uwa ne ko bare, dan gari ne ko bako. Wato dai duk ta kan wanda gaskiya ta biyo a fade ta. Wannan shi ne adalci a shaida, kuma shi ne babbar alamar tsoron Allah.
4.     “Lallai Allah Yana umarrni da adalci da kyautatawa da ba ma’abota kusanci hakkinsu. Kuma Yana hani daga alfasha da ayyukan ki da zalunci. Yana yi muku wa’azi ko za ku fadaka.” (Suratul Nahli:90).
Ita ma wannan ayar tana dada nanata umarnin Allah Madaukai ne game da yin adalci da kuma kyautatawa. Kyautatawa ita ce matsayin adalci mafi kololuwa. Wato ma’anar kyautatawa ya hada da yafiya ko yi wa mutum kari a bisa iya abin da ya cancanci samu ko mallaka. Kyautatawa a janibin Ubangiji kuwa, shi ne mutum ya aikata ayyukan ibadar da ba a wajabta masa ba, ko kuma ya bar abubuwan da ba a haramta masa yin su ba. Wato kamar barin makaruhi da shubha da makamantansu. Ko kuma kamar yin nafiloli da azumin tadawwa’i nafila) kuma kyautatawar Ubangiji ga bayi, ita ce gafararSa da afuwarSa da rahmarSa da jinkanSa da tausayinSa da tausasawarSa da hakurinSa da kuma cetonSa ta hanyoyi daban-daban ga managartan bayi da masu sabo, don su yi nadama su daina.
5.     “Ku yi adalci. Lallai Allah Yana son masu adalci.”  (Suratul Hujurat:9)
Wannan ayar tana tabbatar da cewar yin adalci, kan sanya bawa ya kai matsayin shiga cikin bayin da Allah Yake sonsu. Wanda kuwa har ya kai matsayin da Allah Madaukaki Yake kaunarSa, to tabbas ana yi masa fatar samun rahamar Ubangiji a nan duniya da gobe kiyama.
Ma’anar adalci shi ne aikata daidai ta fuskar furuci da aiki gwargwadon bukatuwa, ba tare da tawaya ko zakewa ba, ga wanda ka sani ko wanda ba ka san shi ba, ko makusanci ko na nesa, ko wanda kuke addini daya ko bare, da sauran makamantansu. Daga cikin dabi’un da suke nanike da adalci, akwai gaskiya da amana da cika alkawari. Babu in da za ka ga adalci sai ka gan su. Kuma babu in da za ka gan su, sannan ya zamana babu adalci a wurin. Don haka ana fahimtar adalcin mutum ne ta hanyar gaskiyarsa a furuci da aiki da amanarsa a furuci da aiki da kuma cika alkawarinsa a furuci da aiki. Haka kuma duk wanda ya rasa wadannan dabi’u uku, to kada ma a nemi adalci a tare da shi. Wanda ya rasa wata dabi’a daga cikin ukun, to adalcinsa tauyayye ne.

Adalci tsakanin bawa da Allah:
Adalci a tsakanin bawa da Allah shi ne ya bauta maSa Shi kadai, kada ya yi masa tarayya a bauta ko siffofinSa ko matsayinSa ko kuma a duk wani abu da ya kebantu da Shi a zatinSa. Mutum ya bi Allah gwargwadon iyawarsa, sannan ya bar sabon Allah matukar iyawarsa, ya gode maSa bisa dukkan ni’imomi da falalolin da Ya yi masa a bayyane da boye.
Adalci a hukunci:
Shi ne shugabanni da jagorori da wakilai da kuma alkalai, su tabbatar sun ba duk wani mai hakki hakkinsa. Wato kowane mutum a ba shi abin da ya cancance shi na sakamako ko rabo ko taimako ko tallafi gwargwadon abin da ake da shi, kuma a a bisa tsarin da aka yarda a gudanar, a lokacin akwai da lokacin babu, a lokacin yalwa da lokacin tsanani, a lokacin samu da lokacin nema da kuma lokacin kwanciyar hankali da lokacin matsaloli.
In ka cire imani, to babu dabi’ar da ta kai adalci, muhimmanci a rayuwar dan Adam. Domin adalci ne kawai ke sanya a fifita zabin adalin kafiri shugaba a kan azzalumin shugaba Musulmi. Kuma shi Musulunci yana umarni da dora adalai a duk wata sabga ta shugabanci ko wakilci ko kuma rikon amanar dukiya ko harkokin jama’a. Don haka adali ya fi mai yawan ibadar da ba ya da adalci, ko malamin da ba ya da adalci, ko kwararren da ba ya da adalci.
Adalci shi yake gyara komai, ya daukaka kowa, kuma ya yalwata alheri a cikin al’umma. Adalan shugabanni da jagorori da wakilai da malamai da alkalai da kwararru su suke kawo gyara na alheri. Kuma su iya ciyar da al’umma ga matsayin daukaka da aminci.
Idan kuwa har aka rasa adalci a tsakanin daidaikun jama’a da a al’ummance da kuma a hukumance, to komai zai dagule, lamura za su cakude, mutane za su rikice, mulki zai ruguje, kuma zaman lafiya zai gagara.